1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaAfirka

Hisbah tana keta hakkin dan Adam

Nasir Salisu Zango SB
March 13, 2024

A Kano da ke Najeriya Hisbah ta kai sumame wuraren sayar da abinci da rana tare da kama masu sayar da abincin da wadanda aka samu suna cin abinci lamarin da masana a fannin sharia ke cewar keta alhakkin dan Adam ne.

https://p.dw.com/p/4dTYt
Najeriya | Kano | Hukumar Hisbah
Hukumar Hisbah ta KanoHoto: AFP/AMINU ABUBAKAR

Da ma dai duk shekara warhaka 'yan Hisbah a Kano kan fita sumame domin kamen mutanen da ake gani suna cin abinci da rana, sai dai masana a fannin shari'a da masu kishin al'umma na ganin cewar wannan mataki tamkar keta hakkin bani Adama ne na mutane. Da yawan wadanda ake kamawa na cewar rashin lafiya ke damun su, wasu kuma na cewar su dama sai sun ga wata suke dauka kuma haka suka taso ana yi a danginsu iyaye da kakanni.

Karin Bayani: Kano: Sulhun gwamna da Daurawa

Malam Aminu Khidir malami ne me wa'azi a Kano, ya ce wajibi ne idan ance an ga wata mutum ya dauka amma matafiya na da uziri. Shikuwa Aliyu Dahiru mai fashin baki kan al'umuran yau da kullum ya bayyana cewar wuce makadi da rawan ne ke sa ana kamen wadanda ba sa azumi, yi wa addini shishshigi ne, domin zamanin ma'aiki ba a yi ba

Umar Usman Danbaito, lauya mai zaman kansa a Kano ya ce babu wata doka da ta yi tanadin kamen masu azumi dan haka kundin tsarin mulkin Najeriya sashi na 36 ya hana shigarwa dan Adam hanci da kudundune. Hukumar Hisbah dai tana cewar tana daukar matakin ne a matsayin umarni da aiki mai kyau da hani ga mummuna, sai dai da yawan mutane na cewar an saba lamba.