1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kalubalen da ke gaban sabbin mahukunta a Mali

September 29, 2020

Bangarori dabam-dabam a Mali na tofa albarkacin bakinsu kan muhimman kalubalai da ke gaban shugaban majalisar ministocin kasar da suka hada da rikicin siyasa a cikin gida da matsalolin tsaro.

https://p.dw.com/p/3jBaQ
Firaministan wucin gadi na kasar Mali, Moctar Ouane, da zai jagoranci gwamnati tsawon wata 18
Firaministan wucin gadi na kasar Mali, Moctar Ouane, da zai jagoranci gwamnati tsawon wata 18Hoto: Louafi Larbi/Reuters

A yanzu dai a bayyane take cewa tsohon ministan harkokin wajen Mali da ke da alhakin jan ragamar majalisar ministocin gwamnatin wucin gadin kasar ka iya fuskantar tarin kalubalai na cikin gida, kama daga batun rikicin siyasar da shi ne ma silar yiwa gwamnatin Ibrahim Boubacar Keita juyin mulki da na zamantakewa tsakanin 'yan kasar mai fama da rikice-rikicen kabilanci, baya ga na tsaro da na tattalin arziki da na kiwo lafiya.

Sai dai a ganin Moussa Sidibe wani mai fashin bakin siyasar kasar kamata ya yi sabon firaministan ya soma kaddamar da binciken yadda gwamnatocin da suka shude suka tafiyar da mulkinsu na wa'adin shekaru 20 da suka gabata domin bankado wadanda suka yi cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arzikin kasar zagon kasa.

"Duk wata badakalar yin rub da ciki da dukiyar kasa da 'yan jarida suka bankado ba tare da an yi shari'a a kanta ba, kamata ya yi a dawo da ita don jama'a su ga fari, domin har yanzu jama'a na da kishirwar jin abubuwan da suka faru na cin hanci, domin sun jima suna ganin ana ta bayanai kan yaki da cin hanci ba tare da ganin wasu matakai ba a zahiri."

Wakilan kungiyar adawa ta M5-RFP a gun tattaunawa da sojojin da suka yi juyin mulki
Wakilan kungiyar adawa ta M5-RFP a gun tattaunawa da sojojin da suka yi juyin mulkiHoto: AFP/A. Risemberg

Ko baya ga wannan dai har yanzu 'yan Mali na jiran jin sakamakon karshe na dage takunkuman da kungiyar Ecowas ta kakaba wa kasar mai fama da talauci da fatara, ko da yake a cikin watan Afrilun da ya gabata asusun bayar da lamuni na duniya ya ware dala miliyan 200 a matsayin tallafi na farfado da tattalin arzikin kasar.

Karin bayani: Sojojin Mali na neman sasantawa da ECOWAS

Ko da yake ga masu nazari kan harkokin da ka je su komo a kasar na bayyana cewa lamura ka iya rincabewa a 'yan kwanakin da ke tafe musamman ma idan har gwamnatin wucin gadi ba ta yi biyayya ga yarjejeniyar mutunta ayar doka mai lamba 39 da ke magana kan ingancin biyan ma'aikatan kasar albashi ba.

Amadou Coulibaly sakataren kungiyar malaman makaranta ne da ke koyarwa a makarantun firamare mai suna Syneb.

"Akwai dambarwa fiye da yadda ba ka zato da ke jiran gwamnatin nan ta fannin kungiyoyin kwadago, mun rattaba hannu kan yarjejeniya da su idan kuma har yanzu ba a mutunta yarjejeniyar ba a cikin albashinmu na watan gaba to ba shakka za mu shiga yajin aiki wannan ba makawa."

Shugaban kasa na wucin gadi Bah Ndaw lokacin rantsar da shi a birnin Bamako
Shugaban kasa na wucin gadi Bah Ndaw lokacin rantsar da shi a birnin BamakoHoto: Amadou Keita/Reuters

Batun kundin tsarin mulki da hukumomin da ke karkashinsa na daga cikin muhimman batutuwan da ke jiran sabon Firaminista Moctar Ouane duba da yadda zaben 'yan majaklisar dokokin kasar da kotun koli ta kundin tsarin mulkin Mali ta tabbatar ya kasance babban mafari na hayaniyar siyasa a kasar, to amma a ganin Ibrahima Sangho wani kwararre ta fannin zabe a Mali ba nan gizo ke saka ba.

"Sake nazari kan tsarin dokoki takwana shi ne mafi a'ala musamman ma kotun tsarin mulki wacce kudin tsarin mulki na 25 ga watan Fabrairun 1992 ya baiwa cikakken karfin iko. Idan muna da muradin samun hukuma daya mai cikakken iko da za ta lura da harkokin zabe dole sai an sake nazari kan tsarin da kundin tsarin mulki ya tanada."

Gwamnatin dai za ta shafe tsawon watanni 18 ne a matsayin na wucin gadi kana kuma matasa na daga cikin wadanda ke jiran tsammanin ganin an dama da su a cikin tafiyar kamar yadda kungiyoyinsu ke cewa. Sai dai a cewar masanin kimiyar siyasar nan Moussa Sidibé gwamnatin kamata ya yi ta samar da tubali mafi inganci wanda kuma ya danganta ne da zubin tsarin 'yan majalisar ministocinsa.