SiyasaAfirka
Sojoji na son ECOWAS ta cire wa Mali takunkumi
September 22, 2020Talla
A bayaninsa na wannan Talata Kanar Goita ya ce tun a jiya Litinin an nada shugaban gwamnatin riko kuma ya kamata kasashen na kungiyar ECOWAS su sakarwa kasar mara domin ta ci gaba da samun bunkasa.
Dama dai tun farko kungiyar kasashen Afirka ta Yamma ta ECOWAS ta lashi takobin ba za ta janye takunkumin da ta sanya wa kasar Mali ba har sai sojojin sun nada gwamnatin rikon kwarya wace farar hula zai jagoranta.