1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali: 'Yan jihadi sun kai hari Timbuktu

August 27, 2023

Hukumomin Timbuktu da ke Arewacin Mali sun sanar da mutuwar wata 'yar karamar yarinya tare jikkatar wadansu mutane biyu a wani hari da kungiyoyin jihadi suka kai wa birnin.

https://p.dw.com/p/4VcI4
Mali: 'Yan ta'adda sun kai hari TimbuktuHoto: ROMARIC OLLO HIEN/AFP/Getty Images

Wasu majiyoyi sun ce 'yan jihadin masu alaka da kungiyar 'yan tawayen Abzinawa ta Azawad mai fafutikar raba Mali gida biyu sun kai harin da kimanin karfe biyar da rabi na Yammacin Asabar (26.08.2023) inda suka harba rokoki i zuwa birnin. Guda daga cikin rokokin ta fado a kusa da wata kasuwa, lamarin da ya yi ajalin yarinyar mai shekaru 11 da haihuwa.

Karin bayani: Rikici tsakanin 'yan tawaye da gwamnatin Mali

Harin na zuwa ne bayan sama da makonni biyu da kungiyoyin jihadin suka yi garkuwa da birnin na Timbuktubu mai bumbin tarihi bayan da sojojin gwamnati na FAMA suka fatattakesu daga birnin Ber da ke a tazarar kilomita 60 bayan gwabza kazamin fada.

Timbuktu dai na daya daga cikin manyan biranen Arewacin Mali da suka fara fada hannun kugiyoyin jihadi bayan barkewar rikicin kasar a shekarar 2012, inda suka yi kaca-kaca da kayan tarihin birnin tare kuma da shinfida dokkokinsu. 

Karin bayani: ICC: Al Faqi zai biya diyyar hubbaren Timbuktu