1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Malaman addini sun gana da sojin Nijar

Binta Aliyu Zurmi
August 13, 2023

Tawagar malaman addini daga tarayyar Najeriya ta kai ziyarar neman sulhu a jamhuriyar Nijar, inda ta sami tarba ta musamman daga sabon Firaministan kasar.

https://p.dw.com/p/4V6xi
Niger, Niamey | General Mohamed Toumba bei einer Kundgebung von Anhängern der Putschisten
Hoto: Balima Boureima/AA/picture alliance

Ziyarar neman sulhu karkashin jagorancin Sheikh Bala Lau shugaban kungiyar Izallah ta Najeriya, ta gana da shugaban kasar  Abdourahamane Tchani kuma sun bayyana masa da amincewar shugaban Najeriya suke tafe.

A karon farko tun bayan jyuin mulkin, sabuwar gwamnatin soji ta Nijar din ta amince da hawa tebirin tattaunawa da kungiyar Ecowas domin warware rikicin siyasar kasar ta hanyar lumana. 

Sabon Firaiministan Nijar Lamine Zeine ne ya bayyana haka ga manema labarai bayan zama na sama da sa'o'i uku da suka yi.

A daya hannun kuwa hambararen shugaban Nijar Mohammed Bazouum ya sami ganawa da likitansa a jiya, wanda ya tabbatar yana cikin koshin lafiya. Sai dai duk da bukatar malaman Najeriya na neman su gana da shi lamarin ya ta ci tura.