1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makomar Jam'iyyun adawa a Najeriya

October 11, 2024

Kokarin mallakar ruhin jam‘iyyun shekaru biyu kafin babban zabe, daga dukkan alamu ya kasance rikicin da ke barazana ga makomar daukacin jam‘iyyun adawa a Najeriyar a halin yanzu.

https://p.dw.com/p/4lhv0
DW l Kwankwaso Interview, Nigeria
Hoto: Kwankwasiyya official Foto, Kano Nigeria

Jam'iyar adawa ta PDP alal misali, shugabanni biyu ne Ilia Damagun da Ahmed Yayari ke ikirarin halastaccen shugabancin jam'iyyar a mataki tarayya. A yayin kuma da a jam‘iyyar labour Nenadi Usman ke gwada kwanji da Julius Abure. Can ma cikin gidan NNPP akwai ikirarin Abba tsaya da kafarka. Duka a cikin guguwar da ke kara tada hankali a ciki da wajen jam'iyyun.

Atiku ABubakar na Jam'iyyar PDP
Hoto: Radeno Haniel/AP/picture alliance

Komawa zuwa ga Rabbana cikin batun adawar ko kuma farkon Karshen PDP cikin fagen siyasa, In har tsohuwa tana magagin mutuwa, ita ma NNPP da ke zaman kwaila a siyasar ba ta tsira ba a guguwar rigingimun da ke cikin  fagen siyasar.

Can cikin Kano, jiha guda da ke ikon jam'iyyar dai, kai yana rabe a tsakanin masu neman tawaye bisa tsarin da ke gudana a jihar, da kuma masu tunanin dorawa bisa jagorancin Rabi'u Musa kwankwaso. Hashim Suleman shi ne shugaban jam'iyyar NNPP a jihar, kuma yace shedanci ne kokarin raba Abba da mai gidansa na siyasa a jihar. To sai dai in har tarbiyar na nuna alamun karanci cikin fagen siyasa a kasar, sabbabin rigingimun na zaman barazana mai girma a fagen siyasar kasar.

Peter Obi, Bola Tinubu, Atiku Abubakar
Hoto: K. Gänsler/DW, Shengolpixs/IMAGO, EKPEI/AFP

Duk da cewar dai a karon farko an yi nasarar kaiwa  shekaru 25 kan tsarin dimukuradiyya a kasar, rigingimun siyasar dauri ne dai a fadar Farfesa Kamilu Sani Fage da ke zaman kwarrare a batun siyasa suka kai ga zuwa jana'izar tsarin cikin kasar can baya.

Duk da cewar dai sun fi karkata zuwa ga adawa ita kanta APC dake takama da mulkin tarayyar najeriyar dai  ba ta tsira ba cikin jerin rigingimun  da suka kalli kasa kiran taron majalisar zartarwar jam'iyyar na kasa sama da shekara guda. Ko a wannan ranar an dakatar da wasu jiga jigan jam'iyyar da suka hada da minista a jihar Bayelsa