1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rashin tsaro a Najeriya ya yi kamari

Uwais Abubakar Idris LMJ
December 2, 2020

A Najeriya ana mai da martani kan matakin da majalisar dattawa ta dauka na neman shugaban kasar ya kori shugabanin rundunonin tsaro, biyo bayan yadda lamuran tsaron ke kara tabarbarewa.

https://p.dw.com/p/3m7BZ
Nigeria Politik l Senat
Hoto: Getty Images/AFP/K. Sulaimon

Majalisar wakilan Najeriyar dai, na neman karin bayani ne daga Shugaba Muhammadu Buhari dangane da karuwar tabarbarewar tsaro a kasar, wanda ya biyo bayan mummunan harin da aka kai a kan manoma a garin Zabarmari da ke jihar Borno. 

Karin Bayani: Gwamnati za ta magance matsalar tsaro

Sannu a hankali dai tura ta kai bango kuma hakuri na neman karewa a kan yaddaShugabanMuhammadu Buhari na Najeriyar ke tafiyar da harkokin tsaron kasar, domin a karon farko 'yan jamiyyarsa ta APC da ke mulki ne suka jagoranci kudurin da majalisar ta dauka a kansa, abin da ba sabun ba domin a baya har suna aka rada musu na 'yan jeka na yika.


A majalisar dattawa Sanata Kashim Shettima na jihar Borno, ya jagoranci gabatar da kudurin lallai a kori shugabannin rundunonin tsaron kasar don neman samun sauyi. Fusata da bacin rai ya bayyana a fili a majlisar, inda sai da hayaniya ta barke a tsakanin mambobinta kan wannan batu. A karshe 'yan majalisa 13 dukkaninsu daga jam'iyyar APC sun yi uwa da makarbiya kafin majalilisar ta nemi shugaban kasar ya bayyana a gabanta domin yi mata jawabi. 

Nigeria Kashim Shettima, Gouverneur Borno
Hoto: Reuters/A. Sotunde

Karin Bayani: Yawaitar kananan makamai a Najeriya

An dai dade ana kalon kiraye-kirayen 'yan majalisar a matsayin ihu bayan hari. Amma ga Barrsiter Mainasara Umar ya ce, 'yan majalisar su sani fa tasu shawara ce babu dole a kan shugaban ya bi abin da suke so. A bayyane take cewa shugaban na Najeriya na kara fuskantar matsin lamba daga 'yan majalisar dokoki da ma kungiyoyi kamar Afenifere da ta dattawan Arewa da ta kai ga fara kiran ya sauka daga mukaminsa a kan tabarbarewa tsaro da ya kai wa kowa a wuya.