1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karuwar talauci da fifiko tsaknin jama'a

June 22, 2021

A yanzu haka dai duniya na fuskantar tsananin talauci da fifiko tsakanin masu hali da marar gata, da kuma karuwar rashin adalci tsakanin al'umma.

https://p.dw.com/p/3vNGl
Schweiz Genf | Michelle Bachelet, UN-Menschenrechtskommissarin
Shugabar Hukumar Kare Hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya Michelle BacheletHoto: Fabrice Coffrini/AFP/Getty Images

Wannan dai na kunshe ne cikin rahoton Hukumar Kare Hakkin da Adam ta Majalisar Dinkin Duniya da aka fitar yayin wani taron da ya duba al'amuran da suka shafi take 'yancin dan Adam a duniya. Kasar da aka fi mayar da hankali kan karuwar takurawa al'ummarta ita ce Belarus, wace kungiyoyin kare hakkin dan Adam da kasashen yamma suka mayar da hankali a kanta tun bayan zaben watan Nuwambar bara da aka yi zargin tafka magudi. Bayan kammala zaben dai, hukumomi sun fara yin arangama ga wadanda ke boren rashin yi masu adalci a cikinsa.

Karin Bayani: EU za ta dauki mataki kan Belarus

Shugabar Hukumar Kare Hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya Michelle Bachelet ta yi tsokaci kan rikicin na Belarus: "Ana takurawa 'yancin fadin albarkacin baki da yancin yin taruka tsakanin 'yan kasa. Ana muzgunawa jama'a tare da kai samame ga kafafen yada labarai da kungiyoyin farar hula. Abubawan da ke faruwa dai kawai sune tsare mutane da kuma cin zarafin wadanda aka tsare."

Swjatlana Zichanouskaja | belarussische Oppositionsführerin in Polen
Al'ummar Belarus na zanga-zanagr neman sauyiHoto: Czarek Sokolowski/AP Photo/picture alliance

Sakamakon yadda kasashen yamma suka aza kahon zuka kan mahukuntan na Belarus dangane da yadda suke muzgunawa 'yan adawa, ya sa gwamnati a Minsk ta kori duk wasu kungiyoyi ciki har da masu kare hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya. A cewa Bachelet baya ga Belarus haka bain yake a babbar kawarta wato Rasha, inda a can ma batun takurawa al'umma ya yi matukar karuwa gabanin zaben 'yan majalisar dokoki. Rahotonanni sun nunar da cewa gwamnatin Moskow ta riak tsanantawa 'yan adawa kamar yadda a yanzu ta tsare babban dan adawan kasar Alexei Navalny.

Karin Bayani: Navalny ya fara farfadowa daga jinya

Kasar Chaina ma dai ba ta tsira ba kan batun take hakkin dan Adam din ba, inda Majalisar Dinkin Duniya ta bayar da misali kan yadda mahukuntan Bejin ke kama masu zanga-zanga a yankin Hong-Kong. A cewar majalisar, yanzu haka kimanin mutane 100 na daure a gidajen yari sakamkon shiga zanga-zangar kin jin Chaina. Michelle Bachelet ta kuma yi babbar suka a kan yadda mahukuntan na Chaina ke takurawa Musulmi. Batun halin da ake ciki a yankin Tigray na kasar Habasha ma ya yi matukar jan hakalin taron kare hakkin dan Adam din na Majalisar Dinkin Duniya da ke gudana a Geneva. An yi zargin aikata kisan gilla tsakanin bangarorin gwamnatin Habasha da 'yan tawaye. Wani abu da yanzu haka ake ganin ya kara takurawa al'umma a duniya wanda hukumomin wasu kasashe suka yi amfani da shi wajen kara muzgunawa talakawa, shi ne annobar coronavirus.