1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Hong Kong ya dauki sabon salo

Ramatu Garba Baba AAI
August 30, 2019

Rikicin Hong-Kong yanzu haka ya dauki sabon salo a wannan juma'ar bayan an kame jagoran masu zanga-zanga

https://p.dw.com/p/3Olhe
Yayin da aka kama jagoran masu zanga-zangar a Hong-Kong da wasu mutane uku
Yayin da aka kama jagoran masu zanga-zangar a Hong-Kong da wasu mutane ukuHoto: picture-alliance/AP Photo/K. Cheung

Bayan kiraye-kirayen da kasashen duniya ke yi ga Hong-Kong da su gaggauta kawo karshen rikicin yankin da ke kara yamutsa hazo, rikicin yanzu haka ya dauki sabon salo a wannan juma'ar bayan an kame jagoran masu zanga-zangar da wasu mutane uku. 

Masu zanga-zanga kenan da suka cika wani daki da bangaren masu zanga-zangar ke shirin yi wa manema labarai jawabi kan labarin kama shugabansu Joshua Won da aka yi a safiyar wannan Juma'a,  ISSAC CHENG, shi ne mataimakin jagoran, ya soma da bai wa magoya bayan kwarin gwiwa kafin bayanin halin da aka wayi gari ciki yana mai cewa...

"An kama shi bisa zargin gudanar da zanga-zangar da gwamnati ta haramta, shi da wasu masu gwagwarmaya, yanzu dukkansu na hannun jami'ai, mun tabbatar an kama su gabanin gagarumin gangamin da muka shirya a gobe Asabar don kara matsa kaimi, wannan yunkuri ne na son karya lagon masu zanga-zangar dama, amma muna tabbatar musu ba gudu ba ja da baya''

Hongkong Protest Polizei
Hoto: picture-alliance/ANN

Duk da cewa wannan ba shi bane karon farko da jami'an tsaro ke kama Joshua bisa laifin tayar da zaune tsaye a yankin da al'ummarta ke neman sauyi amma kuma kamen na yau gabanin gangamin da suka ce ba a taba ganin irinsa tun bayan barkewar rikicin ba, ya haifar da cece-kuce, wasu na ganin sam bai dace ba a hana jama'a yancin fadin albarkacin bakinsu, amma wata lauya mai kare gwamnati ta ce doka da kuma wani kwamiti da gwamnati ta kafa ya ba ta damar daukar mataki a yanayi irin wannan.


Thena Kung, lawya mai kare gwamnati
"Hukumar ERO, ta bai wa shugabar karfin kama masu laifi, da hana ayyukan kafafen yada labarai masu yada tarzoma ko kakaba dokar hana fita, da kyale da masu zanga-zangar ba tare da hana su ba, tana da hurumin aiwatar da duk wadannan dokokin don kawo karshen rikicin, wanda zai bai wa al'ummar Hong Kong rayuwa cikin zaman lafiya da kwantaciyar hankali maimakon wannan tashin hankalin''

Thena Kung, Lauya mai kare gwamnati
Thena Kung Lauya mai kare gwamnatiHoto: Reuters/T. Peter

Ba kowa ne ya yarda da wannan bayanin ba kamar yadda wannan lauyan mai suna Holden Chow Ho-ding, ya yi bayani ''ya ce bai dace a hana zanga-zanga ba don kuwa babu dokar da ta tanadi hakan'
''Hukumar ERO da aka kafa, ba ta ayyana haramci na 'yancin walwala ba, aikinta ta sa ido kan gangamin, ta kuma tabbatar rikici bai barke ba, a yayin da ta ke kokarin shawo kan tashin hankalin''

Amma kuma wani, Mukaddashin magajin garin yankin gabashin kasar Chiu Chi-keung, ya ce lokaci ya yi da ya dace gwamnati ta dauki matakin hukunta masu take doka.

''Muna kira ga gwamnati da ta samar da kudirin da zai bata damar tuhumar rukunin da ke rufe fuskokinsu a yayin zanga-zanga, ina ganin ya da ce gwamnati ta tanadi matakan da za ta dauka don ganin an hunkunta su don bai da ce ace an barsu suna ci gaba da cin karensu ba babbaka ba, ganin irin ta'asar da zanga-zangar ke haifarwa tattalin arzikin Hong Kong, ya dace a dauki mataki''


Fiye da watanni hudu kenan da barkewar rikicin yankin na Hong Kong, a tsawon lokacin da aka kwashe ana ja-in-ja da gwamnatin, an zargi 'yan sandan kwantar da tarzoma da laifin amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa ma su zanga-zangar neman sauyi, da ke zaman dirshan a sassan birnin.

Lokacin da aka harba wa masu zanga-zangar barkonon tsohuwa a Hong-Kong
Lokacin da aka harba wa masu zanga-zangar barkonon tsohuwa a Hong-KongHoto: Getty Images/AFP/A. Wallace