1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran: An haramta taron tunawa da Mahsa

Abdourahamane Hassane
September 17, 2023

Hukumomi a Iran sun hana iyalan Mahsa Amini gudanar da wani taro na tunawa da cikon shekara daya da mutuwarta.

https://p.dw.com/p/4WQYU
Zina Mehsa Amini
Zina Mehsa AminiHoto: DW

'Yan sanda sun hana mahaifinta fita daga gidansa bayan sun tsare shi na wani dan lokaci, kamar yaddakungiyoyin kare hakkin dan Adam suka bayyana. Mahsa Amini, mai shekaru 22 da haihuwa 'yar asilin Kurdawan Iran, ta mutu  a ranar 16 ga Satumba, shekara ta 2022,  bayan kamata da laifin keta ka'idojin shigar mata, daya daga cikin ginshikan akidar Jamhuriyar Musulunci ta Iran tun bayan faduwar mulkin Shah a shekarar  ta 1979.