1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta saka wa 'yan sandar da'a a iran takunkumi

Abdoulaye Mamane Amadou
September 23, 2022

Kwanaki bayan da zanga-zangar adawa da kisan Mahsa Amini a Jamhuriyar Musulunci ta Iran, gwamnatin Amirka ta kakaba wa rundunar 'yan sandan da'ar Iran takunkumi

https://p.dw.com/p/4HF9s
Flash-Galerie Iran Britische Botschaft
Hoto: dapd

Amirka ta sanya takunkumi kan 'yan sandan gyaran da'a na kasar Iran da ake jin tsoro, inda ta zargesu da cin zarafi da keta haddin matan Iran da kuma keta hakkokinsu na gudanar da zanga-zangar lumana.

Takunkumin wanda ofishin kula da kadarorin ketare da ke zama wani reshe na ma'aikatar kudin Amirka, ya kuma shafi wasu manyan hukumomin tsaron Iran su bakwai.
Matakin na zuwa ne yayin da ake fama da tashe-tashen hankula a kasar ta jamhuriyar musulunci kan rasuwar Mahsa Amini.

Ma'aikatar kudin ta Amirka ta ce 'yan sandan su ne ke da alhakin mutuwar Amini sai dai tuni rundunar 'yan sandan na Iran ta yi Allah wadai da takunkumin.