1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MACBAN: Gyaran tarbiyya da yaki da yaduwar makamai

Uwais Abubakar Idris
March 12, 2024

Shugabanin kungiyoyin Fulani makiyaya a Najeriya sun koka kan matsalar miyagun kwayoyi da yaduwar kananan makamai a tsakanin Fulani makiyaya

https://p.dw.com/p/4dRYg
Nigeria Fulani-Hirten Konflikte
Hoto: Luis Tato/AFP/Getty Images

Shugabanin kungiyoyin fulanin makiyaya na Najeriya da suka fara wannan yunukuri na gyara halayen ‘yayansu ne saboda zargin amfani da miyagun kwayoyi da kuma makamai musamman bayan karuwar matsalar garkuwa da mutane a cikin kasar sun bayyana takaici kan yadda halayyar bafulatani ta chanza daga kunya, kawaici da karamci da aka san su da shi ya zuwa aikata aiyyukan da basu dace ba. Babba Usman Ngelzarma shine shugaban kungiyar Miyetti Allah Macban ta Najeriya.

Wannan shi ne karon farko da ilahirin kungiyoyin Fulani suka taru a wuri guda inda suka shaida wa juna gaskiya a kan wannan matsala ta garkuwa da jama'a. Dr Abubakar Umar Girei shine wakilin Lamidon Adamawa a wajen taron da ya bayyana dabarar da suke son amfani da ita.

A yayinda ake wannan kokari a wani abinda ba'a taba ganin irinsa ba ‘yan bindigar da suka sace 'yan makaranta a unguwar Goni Gora da ke Kaduna sun bukcai a biyasu Naira tirliyan 40 a matsayin kudin fansa a kuma hada masu da motoci Hilux 11 da Babura 150.

Kungiyar Miyatti Allah ta bayyana cewa matsalar garkuwa da jama'a ta yi dalilin salwantar shanu sama da milyan hudu tare da rasa rayyukan makiyaya dubu 15 a Najeriya inda sama da makiyaya dubu 15 suka yi kaura daga Najeriyar