1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An nemi likitoci su koma aiki a Legas

May 21, 2020

Kungiyar likitoci ta kasa a Najeriya (NMA) ta yi kira ga reshenta na jihar Legas da ta janye yajin aikin da ta shiga saboda zargin cin zarafin daga jami'an tsaro musamman ma dai 'yan sanda.

https://p.dw.com/p/3caQl
Symbolbild Apotheke Äquatorialguinea
Hoto: imago/imagebroker

Kungiyar ta NMA ta ce ta shawarci likitocin da sauran jami'an kiwon lafiya kan su koma bakin aikinsu ne bayan wani zama da ta yi da jami'an na tsaro inda suka bada tabbacin kauracewa cin zarafin likitocin.

Gabannin shiga yajin aikin dai, likitocin na Legas sun ce jami'an 'yan sanda kan hanasu sukuni duk kuwa da cewar ba sa cikin rukunin mutanen da aka haramtawa zirga-zirga a jihar saboda takaita yaduwar coronavirus, inda a wani lokaci suka ce 'yan sanda sun tsare wata motar daukar marasa lafiya na wani dan lokaci sannan suka ci zarafin jami'an da ke tare da motar.