1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Zaben Laberiya zagaye na biyu

Zainab Mohammed Abubakar
October 17, 2023

Laberiya na shirin kada kuri'a a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa, tsakanin George Weah da abokin hamayyarsa Joseph Boakai, bisa ga sakamakon wucin gadi.

https://p.dw.com/p/4Xdm3
Liberia Monrovia Parlamentswahlen
Hoto: JOHN WESSELS/AFP

Bayan da aka kidaya sama da kashi 94 cikin 100 na kuri'un da aka kada, Boakai mai shekaru 78 ya samu kashi 43.70, yayin da Weah mai shekaru 57, kuma tsohon dan wasan kwallon kafa na duniya da ke neman wa'adi na biyu, ya samu kashi 43.65 cikin 100 bisa sakamakon da hukumar zaben kasar ta fitar.

Alkaluma sun nuna cewa Weah ko Boakai ba su da isassun kuri'u da zai basu cikakken rinjaye da kuma zabar su a zagaye na farko. Ana shirin gudanar da zagaye na biyu na zaben makwanni biyu bayan bayyana sakamakon hukumance, amma ana iya jinkirta shi ta hanyar daukaka kara.

Kungiyar kasashen yammacin Afirka ECOWAS da kungiyar Tarayyar Afirka sun taya gwamnatin Laberiya da hukumar zaben kasar murnar gudanar da zabe cikin lumana, wanda ya samu fitowar jama'a.