1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Laberiya na zaben shugaban kasa

October 10, 2023

Laberiya na zaben shugaban kasa da kuma 'yan majalisar dokoki, wanda zai nuna makomar shugaban kasar kana tsohon dan wasan kwallon kafa, George Weah da ke neman wa'adi na biyu.

https://p.dw.com/p/4XKZl
Shugaban kasar Laberiya George Weah
Shugaban kasar Laberiya George WeahHoto: Peter Dejong/AP/picture alliance

Daga cikin 'yan takara wadanda ke fafatawa a zaben har da tsohon mataimakin shugaban kasar, Joseph Boakai da ke zama babban mai kalubalantar shugaba Weah. Manyan jami'iyyun siyasar kasar sun yi alkawarin gudanar da zaben cikin lumana a kasar da ke yammacin Afirka. Sai dai arangama tsakanin magoya bayan jami'iyyun kasar a baya-bayan nan na haifar da fargaba a zukanta jama'a.

Karin bayani: Fargaban faruwar tashin hankali a zaben Laberiya

Yaki da cin hanci da karbar rashawa na daga cikin alkawaru da 'yan takara suka yi idan suka lashe zabe, kasancewar laberiya na sahun gaba a kasashen da ke fama da wannan matsala a duniya. Tuni dai aka tura masu sanya ido kan zabe na kungiyoyin Tarayyar Turai EU da Tarayyar Afirka AU da na ECOWAS da kuma Amirka.