1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Weah ya gaza lashe zaben Laberiya

Lateefa Mustapha Ja'afar
October 24, 2023

Hukumar Zaben Laberiya, ta bayyana cewa za a yi zabe zagaye na biyu na shugaban kasa. Wannan dai na zuwa ne bayan da aka kammala kidaya baki dayan kuri'un da aka kada a zaben kasar.

https://p.dw.com/p/4XzB8
Laberiya | George Manneh Weah | Shugaban Kasa | Zabe
Shugaban kasar Laberiya George WeahHoto: Peter Dejong/AP/picture alliance

A yanzu dai za a je zagaye na biyu na zaben shugaban kasa a Laberiyan tsakanin 'yan takarar biyu da ke kan gaba a sakamakon zaben da aka fafata din, wato shugaban kasar mai ci yanzu George Manneh Weah da kuma babban  jagoran adawar kasar Joseph Boakai.