1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Anthony Joshua ya farfado da karfin gwiwa

Suleiman Babayo AMA
April 3, 2023

Dan wasan danben Najeriya Anthony Joshua ya samu nasara kan Jermaine Franklin, a yayin da mai horar da 'yan wasan Chelsea Graham Potter ya yi bankwana da kungiyar

https://p.dw.com/p/4PdG3
Gumurzun  Anthony Joshua da Oleksandr Usyk
Gumurzun Anthony Joshua da Oleksandr UsykHoto: Hassan Ammar/AP/picture alliance

Kungiyar kwalon kafa ta Chelsea a Ingila, ta sallami mai horas da 'yan wasan kungiyar Graham Potter, haka ita ma kungiyar Leicester City ta sallami mai horas da 'yan wasan Brendan Rodgers, lamarin da ke kara nuna rashin tabbas kan korar masu horas da kungiyoyi a wasanin lig na Firimiya da ke gudana. Hakan na da nasaba da irin rashin taka rawar da ake bukata daga masu horas da 'yan wasan.

A wasannin Firimiya Lig, Aston Villa ta bi Chelsea har gida ta doke ta biyu da nema, Arsenal ta doke Leeds 4 da 1, Manchester City ta lallasa Liverpool 4 da 1.

Fafatawar Real Madrid da Barcelona
Fafatawar Real Madrid da BarcelonaHoto: Bernat Armangue/AP Photo/picture alliance

A wasannin lig na kasar Spian La Liga, kungiyar Real Madrid ta yi wa Valladolid cin kacar tsohon keke rakacau, 6 da nema, inda dan wasa Karim Benzima kadai ya jefa kwallaye 3 daga cikin shida. ita kuma kungiyar Barcelona ta bi Elche har gida ta doke ta 4 da nema.

A wasannin Budnesliga, Eintract Frankfurt da Bochum sun tashi 1 da 1, Union Berlin ta lallasa Stuttgart 3 da nema, Wolfsburg sun tashi 2 da 2 Augsburg, haka Freiburg da Hertha Berlin suka tashi 1 da 1, Kolon da Moenchengladbach sun tashi babu jefa kwallo a raga, Bayern Munich ta doke Dortmund 4 da 2, Schalke ta rasa nasara a gida a hannun Leverkusen 3 da nema. Leipzig ta sha kaye a gida a hannun Mainz da ci 3 da nema.

Bundesliga: Wolfsburg da FC Augsburg
Bundesliga: Wolfsburg da FC AugsburgHoto: Bahho Kara/Eibner/IMAGO

Anthony Joshua dan Najeriya ya farfado da karfin gwiwa bayan samu nasara kan Jermaine Franklin yayin damben da ya wakana a karshen mako. Wannan ke zama nasarar da Joshua ya samu a karon farko tun shekara ta 2020 a damben na ajin masu nauyi.

Rashin nasarar Kamaru a fagen tamaula ya janyo mata bakin jini sosai ga magoya bayanta inda ake daura laifin kan mai horaswa da shugaban hukumar wasan kwallon kafar kasar Samuel Eto'o.