1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Shirin kafa sabuwa jam'iyya daga arewacin Najeriya

January 6, 2025

A yayin da ake ci gaba cikin batun siyasa, kungiyar league of Northern Democrat da ke a arewacin Najeriya ta ce tana shirin rikidewa zuwa jam'iyya da ke da babban burin ceto ga 'yan kasar bisa gazawar manya.

https://p.dw.com/p/4orrP
Tutar Najeriya
Tutar NajeriyaHoto: IMAGO/Westlight

 

To sai dai kuma a cikin Najeriya, kuma a fadar kungiyar League of Northern Democrats, ba a gina daukacin manyan jam'iyyun kasar guda biyu ba domin biyan bukatar talakawa na kasar. Kama daga PDP da ta mulki kasar na shekaru dai dai har 16 ya zuwa APC da ke cikin 10 na farko dai, batun son zuciya ne a gaba a wajen rawa da kila ma juyi na daukacin jam'iyyun siyasa na kasar.

Karin Bayani: Kalubalen 'yancin kananan hukumomin Najeriya

Jaridun Najeriya
Jaridun NajeriyaHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP

Dr Umar Ardo dai na zaman jigo a cikin kungiyar ta league of Northern Democrats, da kuma ya ce kungiyar na shirin narkewa ya zuwa jam'iyyar dake da burin ceto kasar. Zama da kishiya sai dole, ko kuma kokari na neman mafita dai, koma ta ina sabbin masu rigar sauyin suke fadin sun gano, sanin asali da kila ma tushe dai ya saka da kamar wuya iya a karba tunaninsu. Ibrahim Abdullahi dai na zaman mataimakin kakakin jam'iyar PDP na kasa.kuma ya ce sabbin 'yan rajin sauyin su suka rusa daukacin jam'iyyun.

Sanata Bala Na'allah jigo ne a kungiyar ta Northern Democrat, kuma ya ce akwai alamun wuce makadi cikin rawa a bangare na kungiyar da a baya ke fadin ba ta da buri na siyasa, amma kuma ke neman rikidewa zuwa sahun gaba a halin yanzu. Abun jira a gani dai na zaman yadda take shirin kayawa a tsakanin masu neman sauyin da masu tunanin sauyin ya tsaya cikin aljihu na kalilan.