1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Kotu ta tura Maina gidan yari

November 9, 2021

Hukuncin daurin shekaru takwas da wata kotun ta yi wa tsohon shugaban hukumar fansho ta Najeriya Abdulrasheed Maina bayan samun sa da laifin satar kudin fansho Naira bilyan biyu ya sanya martani

https://p.dw.com/p/42mzJ
Nigeria Abdulrasheed Maina
Hoto: Federal High Court Abuja

Bayan kwashe shekarau 11 ana tafka shari’a a kan laifi na tsunduma hannu a cikin kudin ‘yan fansho a Najeriya, a karshe kotu ta samu tsohon shugaban kwamitin sake fasalin ‘yan fansho da aka rusa  Abdulrasheed Maina da laifi dumu-dumu na satar kudin ‘yan fanshon har Naira biliyan biyu, laifin da mai shari’a Abang ya yanke masa hukuncin shekaru 61 amma bisa tsari na shari’a zai yi shekaru takwas ne a gidan yari na gyara halinka wanda ya fara daga ranar 20 ga watan Oktoba 2019.  

Hukumar yaki da masu cin hanci ta EFCC ce dai ta yi ta kai gwauro tana kai mari, kafin komarta ta cafke Abdulrasheed duk da kokarin arcewa da ya yi da aka cafko shi a Jamhuriyar Nijar. 

Ci da gumin ‘yan fansho a Najeriya lamari ne da aka dade ana yi, kama daga cusa sunaye na boge zuwa ci gaba da karbar wadanda suka mutu, yayinda rayayyun ake barinsu ba tare da cin gajiyar aikin da suka kwashe shekaru 35 suna yi wa kasa hidima ba. Ko wane tasiri wannan zai yi a kokarin yakar masu halin bera musamman na kudin ‘yan fansho a Najeriyar? 

Baya ga hukuncin daurin  da kotun ta yi wa Abdulrasheed kotu ta umurce shi ya maida wa gwamnatin Najeriya sama da Naira bilyan 1.8 kuma ya yi asarar manyan gidaje da motoci na alfarma da suka hada da Range Rover da BMW.

Ana cike da fatan hukuncin da aka yi masa zai zama misali ga masu aniyar tsunduma hannu a kudin da aka basu amana a Najeriyar da ya kamata su kare.