1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Koriya ta Arewa ta harba makamai masu linzami

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim MAB
September 12, 2024

Japan ta yi tir da gwajin makamai masu linzami na Koriya ta Arewa, wanda ta bayyana a matsayin takalar fada da kuma ta da husuma bayan fadawar wasu kusa da ita

https://p.dw.com/p/4kX99
Hoto: KCNA VIA KNS/AFP

Koriya ta Arewa ta harba makamai masu linzami a gabashin gabar ruwan kasar, wanda ke zama irin sa na farko a cikin sama da watanni biyu, domin zama gargadi ga abokan hamayya, a cewar ta.

Karin bayani:Koriya ta Arewa ta yi wa ta Kudu Kashedi

Makaman wadanda aka harba daga Pyongyang babban birnin kasar da safiyar Alhamis din nan, sun yi tafiyar kilomita 360 kafin fadawa cikin ruwa.

Karin bayani:Koriya ta Kudu na son yaukaka huldar kasuwanci da kasashen Afirka

Wata sanarwa da ma'aikatar tsaron kasar Japan ta fitar, ta yi tir da wannan gwaji, wanda ta bayyana a matsayin takalar fada da kuma ta da husuma a yankin, bayan da wasu daga cikin makaman suka fada kusa da kasarta.

A makon da ya gabata ne dai firaministan Japan Fumio Kishida ya kai ziyara Seoul babban birnin Koriya ta Kudu, da zummar nuna mata goyon baya a rikicinta da Koriya ta Arewa tare da kara karfafa alaka da ita.