1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dangantaka ta yi tsami tsakanin Koriya ta Arewa da ta Kudu

Abdourahamane Hassane
June 10, 2024

Koriya ta Arewa ta sake aika daruruwan balan-balon shara zuwa Koriya ta Kudu, kuma ta yi gargadin cewa za ta dau mataki idan Seoul ta ci gaba da tsokanarta.

https://p.dw.com/p/4gsM7
Hoto: Jeonbuk Fire Headquarters/AP/picture alliance

 Dangantakarda ke tsakanin Koriyar ta arewa da ta kudu, ta yi tsami fiye da goman shekaru. A makwannin baya-bayan nan, Pyongyang ta aike da daruruwan balan- balo cike da shara a wani abin da ta kira kashedi wa Koriya ta Kudun saboda farfagandar da take yi na kasashen yammacin duniya.