1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen yankin Sahel na kokarin dakile ta'addanci

Gazali Abdou Tasawa AH
July 4, 2019

Shekaru biyar bayan kafa rundunar G5 Sahel da nufin yaki da ta'addanci a yankin na Sahel, yanzu haka kungiyoyin 'yan ta'adda na ci gaba da yaduwa da kai hare-hare. Babban sakataren kungiyar ta G5 ya ce da sauran aiki.

https://p.dw.com/p/3LZoa
Mauretanien G5 Sahel Taskforce
Hoto: Getty Images/AFP/T. Samson

Da yake tsokaci a game da yadda aka yi wannan matsala ta tsaro a yankin Sahel ke zama tamkar ana magani kai na kaba, inda kungiyoyin 'yan ta'adda da suka yi kaka gida a arewacin Kasar Mali ke ci gaba da kai hare-hare a kasashen yankin na Sahel musamman a kasashen Mali da Nijar da Burkina Faso,Sakataren dindindin na kungiyar ta G5 Sahel Maman Sambo Sidikou, ya bayyana irin abubuwan da ke yin tarnaki ga tafiyar shirin da ma bukatar sake salon tafiyar da aikin kungiyar yana mai cewa:

"Ya ce matsalar ba a magance matsalar arewacin Libiya ba to ina ganin muna yaudarar kanmu ne idan muka yi tunanin za mu iya shawo kan matsalolin tsaron da ke damuwar yankin namu. Ko da yake cewa wannan matsala ta Afirka da ya kamata 'yan Afirka su magance da kansu, amma abin tambaya shi ne idan har a wasu yankunan duniya da suka fuskanci irin wannan matsala kasashen duniya sun yi taron dangi wajen girka rundunar da ta dakile matsalar, mi ya hana a dauki irin wannan mataki a yankin na Sahel. To amma duk da haka aikin da na yi a rikicin Somaliya ya tabbatar mani da cewa idan muna son yin nasara a cikin wanann yaki to sai mun daina yakin kare kai mun tashi mun kai yaki kai tsaye a wuraren zaman kungiyoyin 'yan ta'addan"

Mauretanien G5 Sahel Taskforce
Hoto: Getty Images/AFP/T. Samson

Sakataren kungiyar ta G5 Sahel Maman Sambo Sidikou ya kara da cewa ko baya ga kasashen na Turai a yanzu kasashen na Sahel sun raba hannunsu biyu inda tuni suka fara samun taimakon kudin sayan kayan aiki daga wasu kasashen irin su Turkiyya da China da kasashen Larabawa da ma wasu kungiyoyin kasa da kasa na Afirka.