Rikicin Boko Haram na nuna alamun lafawa
August 27, 2018Sannu a hankali dai rikicin na Boko Haram na nuna alamun lafawa kuma masu ruwa da tsaki a cikin rikicin na neman sabbin dabarun sake tsugunar da duban ‘yan gudun hijirar da rikicin na ya tagaiyara.
Duk da cewar dai kusan mutane miliyan 40 ne ke rayuwa a kasashe shida da ke kewaye da tafkin Chadi, akalla kusan Miliyan biyu da kusan rabi ne yakin ya raba da gidajensu a wani abun da ke zaman daya daga cikin yanayi na gaggawa mai muni a duniya baki daya.
To sai dai kuma bayan nuna alamun sassautawar rikicin dai kwarraru a ciki dama a wajen yankin sun maida hankali ga kokarin mayar da kowa zuwa gida dama tabbatar da rayuwa mai inganci a cikin yankin.
Wani taro na kwararru da ke gudana a Abuja na nazarin wasu jerin dabaru guda tara da suka hada da sake karfafa imanin al’umma da samar da ayyukan yi dama ilimi a tsakanin mata da maza da yara a daukacin yankin a fadar Bakabe Mouhammadu da ke zama gwamnan Diffa a Jamhuriyar Nijer daya kuma a cikin muhimman cibiyoyin rikicin.
A nasa bangaren Ambassada Nuhu Mamman da ke zaman shugaban hukumar kula da tafkin Chadin, yace agaji na manya da knana na kasashe na duniya zai yi tasiri a kokarin kaiwa ga san barka ga al’ummar yankin.
Sai dai duk da cewar ba’a kai ga tabbatar da yawan kudaden ake da bukata da nufin aiwatar da sabon shirin mai tasiri ba, ana sa rai kungiyar AU dama kasashen yankin zasu samar da kusan kaso 75 cikin dari na kudaden a yayin kuma da ragowar ake shirin samo su a hannun kasashen duniya.
Ambassada Hadiza Mustapha dai na zaman wakiliyar hukumar raya kasashe ta Africa AU.
Abin jira a gani dai na zaman tasirin sabon shirin da ke zama na baya bayan nan da kuma ake fatan sake dora yankin a cikin taswirar ci gaban al’umma.