1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dinke baraka tsakanin Ghana da Najeriya

June 24, 2020

A wani abin da ke zaman yunkurinta na kauce wa sabon rikicin diplomasiyya, kasar Ghana ta nemi gafarar Najeriya bayan rushe wani gini a harabar ofishin jakadancin Najeriya da ke birnin Accra.

https://p.dw.com/p/3eI4M
Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo Addo
Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo AddoHoto: picture-alliance/Photoshot

Dangantaka tsakanin manyan giwaye a cikin yankin yammacin Afirka ta fara sauyin launi da dandano ne bayan rufe iyakar tarrayar Najeriyar da makwabta na kasashe bisa batun tsaro a shekarar 2019.

To sai dai kuma ko bayan cin zarafi na 'yan kasuwar tarrayar Najeriya a manya na birane na kasar Ghana dai abubuwa sun dada cabewa sakamakon rushe wani gini a haraba ofishin jakadancin tarrayar Najeriyar da ke birnin Accra.

Abin kuma da ya bata ran 'yan mulki da ma talakawa na Najeriya da ke masa kallon cin fuska da kokarin cin zarafin tarrayar Najeriyar da ke zaman shugaba a yankin na yammacin Afirka.

Kama daga masana ya zuwa 'yan majalisar tarraya na Najeriya dai sun nemi mayar da martanin da ya dace kan Ghanan da ma kadarorinta da ke cikin tarrayar Najeriya da nufin nunin bacin rai da kila aiken sakon taunin tsakuwa ga tsohuwar kawar a lokaci mai nisa.

Kasashen Ghana da Najeriya na taka muhimmiyar rawa wajen hadin kan kasashen ECOWAS
Kasashen Ghana da Najeriya na taka muhimmiyar rawa wajen hadin kan kasashen ECOWASHoto: Getty Images/AFP/K. Sulaimon

To sai dai kuma wani ban hakuri a bangare na shugaban kasar ta Ghana Nana Akufo Addo na shirin ceton madarar diplomasiyyar da ke tangal-tangal a tsakanin Abujar da kuma Accra.

Wata sanarwar fadar gwamnatin Najeriyar da ta ce ko bayan neman afuwar, kasar ta Ghana na shirin gurfanar da masu laifin rusau din a gaban shari'a na shirin kwantar da hankulan 'yan mulkin na Abuja a fadar Mallam Garba Shehu da ke zaman kakaki na gwamnatin tarrayar Najeriyar.

Kokari na marin juna a tsakanin manya ko kuma kokari na huce haushin kura a kan kare dai, ko a cikin wannan mako 'yan Najeriyar mazauna Accra sun kai ga zanga-zanga ta lumana bayan abin da suka kira hana su gudanar da harkokinsu na kasuwanci a bangare na 'ya'yan Ghanar.

Abin kuma da ya sa a tunanin 'yan dokar tarrayar Najeriyar ake bukatar yiwa tufkar hanci a cikin neman mutunta tsarin juna da kila cin gajiya ta cudanyar junan.

Hon mansur Ali Mashi dai na zaman wani dan majalisar wakilan tarrayar Najeriyar da kuma ya ce ban hakurin hukumomi na kasar ta Ghana bai wadatar ba a kokari na kai karshen matsalar da ke dada sauyi na salo.

Abin jira a gani dai na zaman tasirin rigingimun a cikin tsarin da yake neman tabbatar da gammaya a tsakanin al'ummar yankin na yammacin Afirka miliyan sama da 300.