Kazakhstan za ta rubanya sayar wa Jamus mai
September 28, 2023Kassym-Jomart Tokayev ya fada yayin taron manema labarai da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz a ziyarar da kai Berlin cewa Astana ta samar da metric ton 500,000 na danyen mai ga Jamus ta hanyar bututun Druzhba na Rashaa wannan shekarar ta 2023 bayan da Jamus ta sanar da dakatar da sayen mai daga Rasha.
Karin Bayani: Scholz na son dakatar da sayen man Rasha
Ya baiyana Jamus a matsayin babbar abokiyar kawance a nahiyar turai. Ya kuma gayyaci Shugaban gwamnatin na Jamus Olaf Scholz da ya kai ziyara Astana a duk lokacin da ya ke da ya sami dama.
A nasa bangaren shugaban Jamus Olaf Scholz ya ce Kazakhstan babbar kawace kuma abokiyar kasuwanci a tsakiyar Asiya yana mai cewa shi da Tokayev sun amince su rubanya cinikayya da zuba jari a tsakanin kasashensu.