Kazakhstan za ta tura danyen mai Jamus
February 22, 2023Talla
Ministan makamashi na Kazakhstan Bolat Akchaulakov ya ce yana fatan komai ya tafi daidai a yau.
Makamashin na kasar Kazakhstan zai maye gurbin wanda Jamus ke saye daga Rasha ne tun bayan takunkumai da kasashen yamma suka kakaba wa Rasha bayan mamayar Ukraine da ya dakatar da shigar da man kasar zuwa kasashen yamma.
Danyen man da zai bi ta bututun nan na Druzhba wanda ya fi kowane girma a duniya wanda kuma baya cikin takunkuman da ke kan kayayakin kasar Rasha.
Wannan dai shi ne karon farko da manyan tashoshin tace danyan mai da ke Jamuus za su karbi danyen mai ta wannan bututun.