1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Kasashen Larabwa da musulmi sun bukaci tsagaita wuta a Gaza

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
November 20, 2023

China dai ta nuna goyon bayanta ga shirin samar da kasashe biyu masu cin gashin kansu a matsayin mafita kan rikicin Isra'ila da Falasdinawa

https://p.dw.com/p/4ZA3k
Hoto: Florence Lo/REUTERS

Ministocin kasashen Larabwa da na musulmi sun yi kira da a gaggauta tsagaita wuta a Zirin Gaza, a yakin ake yi tsakanin Isra'ila da Falasdinawa, bayan da tawagar ministocin ta ziyarci Beijin babban birnin China don lalubo hanyoyin kawo karshen yakin tare da shigar da kayan agaji yankin.

Tawagar ministocin wadda yanzu haka take ganawa da ministan harkokin wajen China Wang Yi, ta kunshi ministoci daga Saudi Arebiya da Jordan da Masar, sai Indonesia da Falasdinu da jagororin kungiyar kasashen musulmi ta OIC da sauransu.

Sannan  sun yi kira ga kasashen Yamma da su janye goyon bayan da suke bai wa Isra'ila kan dacewar hare-haren da take kai wa Zirin Gaza da take kira da kare kai.

Karin bayani:Akwai yiwuwar tsayar da aikin jinkai a Gaza

Ko a watan jiya na Oktoba sai da taron ministocin da aka gudanar a birnin Riyadh na Saudi Arebiya ya yi kira ga kotun hukunta manyan laifuka ta ICC da ke Hague da ta binciki Isra'ila kan zargin aikata laifukan yaki a kan Falasdinawan.

China dai ta nuna goyon bayanta ga shirin samar da kasashe biyu masu cin gashin kansu a matsayin mafita kan rikicin Isra'ila da Falasdinawa, in ji ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, sannan ya bukaci kasashen duniya da su hanzarta kai dauki wajen ganin an kawo karshen yakin, tare da agazawa wadanda iftila'in yakin ya shafa.

Karin bayani:Matsayar Jamus a rikicin Isra'ila da Hamas

Isra'ila dai na ci gaba da mayar da martani ne kan harin da kungiyar Hamas da wasu manyan kasashen duniya suka ayyana a matsayin ta 'yan ta'adda ta kai mata a ranar 7 ga watan Oktoban jiya, wanda ya hallaka Isra'ilawa 1,400.