1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Karancin fetur zai hana agaji a Gaza

Zainab Mohammed Abubakar
November 16, 2023

Shugaban hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD a yankin Falasdinawa, ya ce yana da yakinin cewar akwai wani yunkuri na murkushe ayyukan jin kai da take yi a Gaza.

https://p.dw.com/p/4Ywfj
Israel Jerusalem | Preseskonferenz UNRWA-Generalkommissar  - Philippe Lazzarini
Hoto: Mostafa Alkharouf/Anadolu/picture alliance

Philippe Lazzarini ya yi gargadin cewar, mai yiwuwa hukumar ta dakatar da ayyukanta gaba daya saboda karancin man fetur.

Hukumar da ke tallafawa sama da mutane 800,000 da suka rasa matsugunansu a zirinGazada Isra'ila ta yi wa kawanya, ta ce tuni aka rufe da dama daga cikin ayyukanta da suka hada da rijiyoyin ruwa da dama, da wasu cibiyoyin samar da ruwa guda biyu.

Lazzarini ya ce tsawon makonni kenan da kungiyar ta roki da a ba ta damar samun man fetur, wanda a ranar Laraba aka kai Zirin Gaza a karon farko tun bayan fara yakin Isra'ila da Hamas.