1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan wasan Afirka na ba da himma a gasar Paralympics

Aliyu Muhammad Waziri AH
September 4, 2024

Yayin da ya rage kwanaki hudu a kammala gasar Paralympics ta masu bukata ta musamman da ke gudana a birnin Paris na Faransa, kasashen Afirka suna ci gaba da ba da mamaki wajan lashe lambobin yabo a wasannin dabam-dabam.

https://p.dw.com/p/4kHY0
Hoto: Himanot Tirune/DW

Kasar Tunisiya da Moroko sune kan gaba a kasashen Afirka wajen lashe kyautuka inda su ka yi kunnen doki kowace ta ke da lambobin yabo bakwai. Sai kuma Aljeriya da Afirka ta Kudu da su ma kowacce take da hudu. Ita ma dai Najeriya da ta gaza samun ko da kyauta guda a gasar Olympics da aka kammala a watan jiya na Augusta zuwa  ta samu lashe azurfa da tagulla guda guda, lamarin da ya sa masharhancin lamuran wasanni a Bauchi Yahuza Yahaya Doka ya ce tabbas sun daga kima da martabar Najeriya da kuma sauran kasashen nahiyar Afirka a duniya yana mai amfani da wannan azancin maganar.

Tigest ist der erste äthiopische Paralympiker, der eine Goldmedaille gewann
Hoto: Himanot Tirune/DW

'Nakasa a zuci take ba a fili ba, ni a ra'ayina wadannan sun ma fi sauran bangarororin wasanni duba da halin da ake ciki a Najeriya ba kowa za ka tsare ka samu yana mai da hankali ba a kan harkar wasanni ba in ba irin wannan ba. Ka ga daidai gwargwado a yanzu dai sai dai mu ce Allah-san-barka hade da kasashen mu na Afirka musamman bangaren masu bukata ta musamman''

Frankreich Paris2024 | Schwimmwettbewerb bei den Paralympischen Spielen
Hoto: VIRGINIE LEFOUR/dpa/Belga/picture alliance

Maryam Bolaji daga Najeriya tana daga cikin wadanda suka samu nasara a wasan kwallon Badminton inda ta samu tagulla lamarin da kuma ya faranta ran yan kasa masu bibiyar gasar ta Paralympics har ma suke ganin kafin a kai ga kammala gasar akwai yiwuwar Najeriya ta kara samun wasu kyautukan da suka hada da zinare kamar yadda wasu kasashen Afirkan suka samu duk da cewa Abdullahi Kanu yana ganin sai sun kara kwazo.