1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karuwar yi wa Fulani kisan gilla a kudancin Najeriya

Uwais Abubakar Idris
May 13, 2022

Gamayyar kungiyoyin arewacin Najeriya ta bukaci gwamnati da ta dauki mataki a kan ci gaba da dauki dai dai da ake wa Fulani makiyaya a kudancin kasar.

https://p.dw.com/p/4BHeF
Nigreria Fulani-Nomaden
Fulani MakiyayiHoto: AFP/Luis Tato

A Najeriya kungiyar Miyatti Allah ta Fulani makiyaya ta bayyana damuwa a kan  sabbin kashe-kashen da ake yiwa ‘yayanta a yankin kudu maso gabashin kasar da ta kaiga hatta dabobinsu basu tsira ba.


Sake kunno kai na hare-haren da ake kai wa makiyaya da dabbobinsu a yankin  Kudu maso Yammacin Najeriyar ne kungiyar Miyetti Allah ta bayyana da takala ce ta babu gaira babu dalili, inda haka siddabn ta yi zargin ana ci gaba da yiwa ‘ya'yanta dauki dai dai a matsugunnansu da ke sassan Kudu maso Gabashin Najeriya abinda ya sanya su bara da ma daga ‘yar yatsa don mahukunta su san abin da ke faruwa. Domin sun ce kalilan na wadannan hare-hare da ake samun labarinsu a yanayi na kisan mummuke da ake yi. Baba Usman Nagelzarma  shi ne sakataren kungiyar Miyatti Macban ta Fulani makiyaya a Najeriya.

Nigreria Fulani-Nomaden
Kiwo a KadunaHoto: AFP/Luis Tato


‘’Wannan al’amari ne da ke damun kowa a matsayinmu na kungiyar Miyatti Allah ana bin shanu har daji ana kashe su don keta kawai ba don a yi amfani da su ba, yawancin wadanda abin ya rutsa da su sun gudu ne daga wasu rigingimu a Najeriya amma ga halin da suka samu kansu a ciki. To muna kira ga gwamnati ta dauki mataki domin maimakon sauki muna ganin abin fa karuwa yake yi’’


Sake kunno kai na lamarin  ya sanya gamayyar kungiyoyin yankin arewacin Najeriya na CNG sanya baki  kan abin da suka kira fakewa da dalilai na siyasa da zaben 2023 da ya sanya sake bullo da hali na tsangwama da kai hare hare a kan makiyaya da ma matafiya zuwa yankin Kudu maso Gabashin Najeriyar. 
To sai dai ga tsohon gwamnan jihar Imo Sanata Rochas Okoroach ya ce suna tsawatawa da ma sa baki a kan lamarin amma akwai abinda ya kamata jama’a su fahimta daga wannan matsala.

Nigreria Fulani-Nomaden
Jigilar shanu zuwa kudancin NajeriyaHoto: AFP/Luis Tato


Kungiyar Miyatti Allah ta Macban na garagadin hatsarin da ake fsukanta sakamakon yawaitar zubar da jini na bani adama. Gwamnatin Najeriyar dai na mai jaddada cewa tana iyakar kokarinta a kan wannan bala’I da kasha kashen jama’a ba tare da doka ba da ya taso kasar a gaba musamman a dai dai lokacin da ake fuskantara zaben 2023.