1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karuwar barazanar tsaro a tsakiyar Najeriya

Uwais Abubakar Idris M. Ahiwa
December 27, 2022

A Najeriya ‘yan bindigar daji sun kai wani hari mai muni a kauyukan Mashegu da ke a jihar Neja inda suka kashe mutane tare da yin garkuwa da wasu sama da 100.

https://p.dw.com/p/4LSg8
Hoto: Str/Getty Images/AFP

A Najeriya ‘yan bindigar daji sun kai wani hari mai muni a wasu kauyuka da ke karamar hukumar Mashegu ta jihar Neja inda suka kashe mutane hudu tare da yin garkuwa da sama da mutane 100 ciki har da mata da yara saboda gaza biyan harajin da suka sanya wa mutane kafin su kwashe amfanin gonarsu.

Sun dai zama tamkar wata gwamnati a wannan yanki na jihar Neja da ma wasu sassan Najeriyar inda ‘yan bindigar dajin suka sanya haraji a matsayin sharadi na barin manoma su debi amfanin gonarsu a wannan lokaci na kaka. Gaza yin haka ne ta sanya suka afka wa mutanen da ke kauyuka 14 a kananan hukumomin Rafi da Mashegu da ke jihar ta Neja.

Hare-hare na ‘yan bindigar daji a wannan yanki ya zama kusan dan kullum domin da damina ba a huta ba da rani ma wajen kwashe amfani gona haka ake fuskantar lamarin. Duk da cewa gwamnati na bayyana daukar karin matakan tsare lafiyar al'umma daga ‘yan bindigar a dajin da ke wannan yanki na jihar.

Nigeria | Schulkindern entführt
Hoto: AP/picture alliance

Kauyukan da abin ya shafa dai sun hada da Mulo da Gidan Malam da Mutum Daya da sauyan yankuna 14 da ke a wadannan kananan hukumomi guda biyu na Rafi da Muriga. Yanayin da ya ta da hankalin jama'a a daidai lokacin da ake tarba-tarba a kan tsadar abinci da ma fuskantar karancinsa a Najeriyar.

Jihar Neja da ke arewa maso tsakiyar Najeriya na cikin jihohin da ke fama da ‘yan bindigar daji saboda makwabtaka da take yi da jihohin Kaduna da Zamfara, abin da ke ta da hankali saboda kusacin ta da Abuja hedikwatar gwamnatin kasar.