1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Dogayen layuka a gidajen mai

May 30, 2023

Bayan da sabon shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetir, masu gidajen mai a Jihohin Katsina da Zamfara sun fara rufe gidajen man.

https://p.dw.com/p/4RyJH
Gidajen mai a Abuja
Gidajen mai a AbujaHoto: AFOLABI SOTUNDE/REUTERS

Sakamakon daukar mataki cire kudaden tallafin a kan man fetir da sabuwar gwamnatin Najeriya ta yi, gidajen man da yawa sun rufe, yayin da wadanda ba su rufe ba, suka kara wa man kudi abin da ya sa ake ci gaba da fuskantar layukan ababan hawa a gidajen man. Al'umma dai na ci gaba da kokawa gami da martani kan matsalar. A jihohin da aka ci sa'a gidajen man sun bude kowanne kan sayar da man a kan frashin da ya ga dama kama daga Naira 240 zuwa 300, 340 zuwa da 500. Sai dai a cewar masana tatttalin arziki irin su Dr Murtala Abdullahi Kwarai malami a sashen nazarin tatttalin arziki na Jami'ar Umaru Musa Yar'adua da ke Katsina cire tallafin man shi ne mafita ganin yadda wasu kalilan ne masu halin bera ke cin ganimar tallafin. Fargabar da al'umma ke yi shi ne bayan cire tallafin man ba lallai ba ne abin da za'a bullo da shi ya amfani al'umma kai tsaye ba, saboda gudun fadawa 'yar gidan jiya wasu su yi babakere da tsarin.