1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karancin abinci ya sa Nijar neman agaji

Gazali Abdou Tasawa MAB
March 10, 2023

Gwamnatin NIjar ta gabatar wa kungiyoyin agaji na kasa da kasa da kundi na jerin hanyoyin tinkarar matsalar karancin abinci sakamakon gardamar damina a wasu yankuna na kasar.

https://p.dw.com/p/4OWTf
Dakoro na cikin garuruwan da suka saba fuskantar karancin amfanin gona a NijarHoto: Daniel Berehulak/Getty Images

Firaministan Jamhuriyar Nijar Ouhoumoudou Mahamadou ya bayyana cewar mutane sama da miliyan biyar ne ke bukatar taimakon abinci a kasar a wannan shekara ta 2023. A Jawabin da ya yi a taro na birnin Niamey, ya bayyana shirin da gwamnatin ta yi na tinkarar wannan matsalar ta hanyar kudin da ta tanada da kuma wanda take bukata daga bangaren Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin agaji na kasa da kasa.

Niger | Ouhoumoudou Mahamadou
Firaministan Nijar Ouhoumoudou Mahamadou Hoto: PNDS Tarayya Partei

Ya ce " Tsarin da kasa ta yi ya tanadi kawo agajin ga mutane miliyan biyu a matsayin rigakafi daga watan Janairu zuwa Mayu ga wasu mutanen miliyan biyu da dubu 872 daga watan Yuni zuna na Agustan wannan shekara. Wannan aiki na bukatar kudi kusan miliyan dubu 264 na CFA. Domin taimaka wa jama'a da abinci da kuma abinci mai gina jiki ga yara da mata masu juna biyu. Za a sayar wa jama'a da abinci a farashin ragon Malam, wasu a raba masu kudi a kyauta. Kazalika za a taimaka wa manoma da kayan noma, da kuma abincin dabbobi tare da aiwatar da nazarce-nazarce masu muhimmanci domin tantance bukatun jama'a na abinci da kuma abinci mai gina jiki. Kuma a cikin wannan mawuyacin hali da muke ciki, na tabbata cewa ku aminnan huldarmu ba za ku yi kasa a gwiwa wajen kawo mana dauki ba."

Nijar ta saba mika kokon bara kan karancin abinci
Shekaru biyar kenan da Nijar ke irin wannan taro da Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin agaji na kasa da kasa inda take gabatar masu da matsalolinta da kuma yin shelar neman agaji daga gare su. Sai dai a yayin da take jawabi a taron, jagoran Kungiyar Tarayyar Turai a Nijar Louise Auben ta ja hankali kan matsalolin da suka dabaibaye Nijar da ke bukatar taimakon jin kai daga kungiyoyi.

Burkina Faso I Flucht und Migration
'Yan gudun hijira na cikin mawuyacin hali a Nijar, a cewar Kungiyar Tarayyar TuraiHoto: Boureima Hama/AFP

Ta ce: "Wannan taro na zuwa ne a cikin muwacin yanayi na tsaro da jin kai, inda matsalar tsaro ke kara kamari a kasashe makwabta. Fararen hula na cikin halin tagayyara inda suke fuskanta kwace da samame da ma kisan gilla. A wannan yanayi ya zama dole ga kungiyoyin agaji su taimaka wa Nijar. Akwai mutane sama da dubu 650 da aka tilasta wa barin matsugunansu, daga cikin sama da dubu 300 'yan gudun hijira ne na cikin gida, a yayin da wasu 'yan gudun hijira kimanin dubu 300 daga kasashe makwabta da ke samun mafaka a Nijar. A yanzu haka, ana ci gaba da fuskantar kwararar 'yan gudun hijira a Jihohin Diffa da Tillabery da Maradi da Tahoua a sakamakon tashe-tashen hankula".

Bayan gabatar da kundayen tsarin gwamnatin Nijar na fuskantar matsalar karancin abinci da ta sauran bala'o'i a wannan shekara ta 2023, kungiyoyin agajin da sauran kasashe aminnan Nijar sun sha alwashi kawo goyon baya ga shirin kamar a shekarun baya.