1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

APC: Tsaka mai wuya neman mataimakin shugaba

Uwais Abubakar Idris SB
June 10, 2022

Manya da kananan jam'iyyun Najeriya sun shiga kalubalen neman 'yan takara a zaben shugaban kasa da gwamnoni amma kalubalen ya fi zafi ga Bola Tinubu dan takara a jam'iyyar APC mai mulki.

https://p.dw.com/p/4CXDs
Nijeriya jam'iyyar APC, Bola Tinubu
Bola Tinubu dan takara a zaben shugabancin Najeriya na jam'iyyar APCHoto: Stefan Heunis/AFP/Getty Images

A lokacin da ‘yan takara kan neman shugabancin Najeriya a jam'iyyun siyasun kasar musamman na APC mai mulki da PDP ta ‘yan adawa ke cikin kalubale na zabo mataimakansu a takara na zaben 2023, hukumar zaben kasar ta ba su wa'adi na mako guda su mika sunayen mataimakansu a matakin shugaban kasa da gwamnonin jihohi domin kammala shirin zaben.

Karin Bayani: Zaben fidda gwani ya bar wasu 'yan siyasa cikin zullumi

Jam'iyyun siyasun Najeriyar musamman na APC da ke mulkin Najeriyar da PDP ta ‘yan adawa na fuskantar kalubale a kan mutanen da za su zabo a matsayin mataimakan ‘yan takara neman shugabancin Najeriya. A jam'iyyar APC mai mulki dai gwamnaonin jam'iyyar da suka yi uwa da makarbiya wajen ganin an zabi Bola Ahmed Tinubu sun yi kakagida a lamarin, inda bayanai ke nuna alkawari ne a tsakani na ya dauki daya daga ciki a matsayin mataimakinsa. A jamiyyar PDP ma dai waka iri daya ce ake rerawa a kan wanda dan takara Atiku Abubakar zai dauka a matsayin mataimakinsa. Mallam Bashir Baba mai sharhi a kan al'muran yau da kullum ya ce lamarin na da sarkakiyar gaske.

Hada hatuna | Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Rabiu Musa Kwankwaso da Atiku Abubakar
Bola Tinubu da Rabiu Musa Kwankwaso da Atiku Abubakar 'yan takara a zaben shugabancin Najeriya na 2023

Tuni dai batun addini da bangaranci ya bayyana a kan batun zabo wane ne zai zama mataimaki ga ‘yan takara na neman shugaban kasa na jamiyyar APC mai mulki da PDP, inda aka ambato tsohon sakataren gwamnatin Najeriya David Lawal Babachir jigo ga yakin neman zaben dan takara na neman shugabancin Najeriya a jam'iyyar APC Bola Tinubu na cewa ahir da maganar dan takara Musulmi mataimakinsa Mususlmi. Dr Kabiru Lawanti na jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria ya na ganin sai an yi a hankali kan batun addini da kabila da ke tasiri a lamarun kasar.

To sai dai ga David Lawal Babachir tsohon sakataren gwamnatin Najeriya kuma jigo a yakin neman zaben dan takarar neman shugaban kasa a jamiyyar APC ya bayyana abin da yasa ‘yan siyasa ke zarya na bin dan takara a siyasar da ke kadawa.

A halin da ake ciki hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya ta bai wa duk jam'iyyun siyasun kasar wa'adin nan da ranar 17 ga watan nan su mika mata sunayen mataimakan ‘yan takara neman shugabancin Najeriya yayin da gwamnoni kuma wa'adinsu nan da ranar 15 ga watan nan don mika sunayen mataimakan ‘yan takara neman gwamna a kasar.