Kaduna: Matashiya mai sarrafa da 'ya'yan itace
April 20, 2022Talla
Ita dai matashiyar Aisha Adamu Ladan ta ce wannan sana’ar ta sayar da 'ya'yan itatuwa ta zo mata a kan kari domin lokaci ya zo da al'umma da dama sun fara yin bankwana da tsoffin irin shayin da suke sha, sun fara komawa amfani da na gargajiya fiye da na sauran shayin zamani da ake kawo su daga kasashen ketare.
A cewarta dai akwai nasarori masu tarin yawa da ta samu, wadanda ke taimaka wa rayuwarta. Kalubalen da ta ce take fuskanta shi ne na rashin kayayyyakin sarrafa wadannan 'ya'yan itatuwa a zamance.
Bayan kammala karatu a kwalejin horar da malamai ta kasa, matashiyar ta kirkiri kamfanin sayar da garin goroba da taura da magarya tare da sauran ‘ya’yan itace na gargajiya da ake yin shayi da su.