Shekara guda da mulkin Joe Biden
January 20, 2022Joe Biden ya samu nasara a zaben da kuri'u fiye da kaso 81 cikin 100, nasarar da ba wani shugaban Amirka da ya taba samu. To ammma watanni 12 kacal a kan mulki, farin jinin shugaban dan jam'iyyarDemocrat ya ragu. Kama daga yadda yake kokarin tabbatar da manufofinsa a majalisa da hauhawar farashin kayyaki, zuwa annobar corona duk sun yi tasirin sauko da marmarin da ake wa Biden daga mataki 54 cikin 100 zuwa 41 cikin 100. Virginia Sapiro farfesa ce a jami'ar Boston, ta yi karin bayani kan mulkin na Biden: "Ban san wani shugaban da ya karbi mulki ya tarar da tarkace masu tarin yawa, kuma yake kokarin kawar da abubuwa a lokacin da Amirkawa ke bukata ba. Hakika ya yi nasara sosai a wasu dokoki, amma mutane ba sa kula sosai."
Karin Bayani: Al'umma na zaman dar-dar bayan kammala zabe a Amirka
A cikin 'yan kwanakin nan rashin zartar da sauye-sauyen hakkin jefa kuri'a da manufar tilasta riga-kafin cutar corona ga manyan 'yan kasuwa, na nufin cewa a cikin 2022 matsalolinsa sun kara ta'azzara. 'Yan jam'iyyarsa ta Democrat sun fito fili sun ce dabarun shugaba Biden na gazawa, kuma sun yi kira da a dauki sabon salo. Sai dai duk da haka Brett Stephens mai sharhi a jaridar New York post, na ganin akwai jan aiki a gaban jam'iyyar Republican. Tsohon shugaban Amirka Donald Trump ya kammala wa'adin mulkinsa bayan ingiza magoya bayansa yin kutse a ginin majalisar dokokin kasar Capitol, ya kuma fice daga fadar White House ba tare da halartar rantsar da Joe Biden a matsayin sabon shugaba ba.
Jim kadan bayan ayyana Biden a matsayin wanda ya yi nasara, mutane da yawa sun yi farin cikin shan kayen tsohon shugaban ksar Donald Trump fiye da murnar nasarar Biden. Daya cikin jigon yakin neman zaben Biden shi ne sake hada kan 'yan kasar, ya kuma sake nanata kalmar hadin kan har sau bakwai a jawabinsa na rantsuwar kama aiki. Amma duk da haka, siyasar bangaranci ta ci gaba. 'Yan jam'iyyar adawa ta Republican sun ci gaba da hana Biden tabbatar da manufofinsa a Majalisa, ya kuma kasa shawo kan Sanatocin Democrat biyu masu rike da madafun iko, su amince da tsarinsa na zuba makudan kudi a bangaren sauyin yanayi da karfafa harkokin kiwon lafiya da sada zumunta.
Karin Bayani:
A gefe guda yawancin masu ra'ayin mazan jiya a kotun koli, na iya dawo da hakkin zubar da ciki daga baya a wannan shekara. A halin da ake ciki kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna cewa har ya zuwa yanzu, kaso 45 cikin 100 na masu kada kuri'a 'yan jam'iyyar adawa ta Republican da ke marawa tsohon shugaban kasar Donald Turmp baya, sun yi imanin cewa an tafka magudi a zaben shugaban kasa. Ga masu sa ido daga wajen Amirka kuwa, jerin al'amura na iya yin fice sama da sauran. Janyewar dakarun kasar daga Afghanistan, ya bai wa Taliban damar karbe mulki ta hanyar rusa shugabancin dimukuradiyya da rugujewar 'yancin dan Adam musamman mata.