1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekara guda da zanga-zanga a majalisar Amirka

January 6, 2022

Batun mika mulki cikin ruwan sanyi a Amirka na da matsayi a tsarin kasar da duniya ke koyi. Sai dai yamustin da magoya tsohon Shugaban Amirka Domald Trump suka yi a majalisar dokoki a ranar 6 ga watan Janairun bara.

https://p.dw.com/p/45DUW
Visual Story 1. Jahrestag der Erstürmung des Kapitols
Hoto: Spencer Platt/Getty Images

Sama da shekaru 200 da suka gabata, kuri'a da ‘yan majalisa ke kadawa a majlisar dokoki domin amincewa da zaben shugaban kasa a Amirka, al'ada ce ta samun sahalewar majalisa da aka saba da ita.

Sai dai ranar shida ga watan Janirun shekarar da ta gabata, ta kasance wani lokaci na juyayi da kuma fadakarwa, abin da masu nazarin al'amura suka ce ya motsa ginshikin dimukuradiyyar kasar.

Visual Story 1. Jahrestag der Erstürmung des Kapitols
Hoto: Alex Edelman/AFP/Getty Images

Yayin da ‘yan majalisar dokoki ke taro domin tabbatar da zaben Shugaba Joe Biden a baran, tsohon shugaban Amirka Donald Trump ya yi wani taron magoya bayansa, dandazon kuwa da ya hada da masu tsananin ra'ayin rikau, suka kwashe makonni suna jayayya da zaben kasar na 2020.

A yunkurinsu na kwace abin da suka kira zaben da aka sace musu, dandazon magoya bayan na Donald Trump suka aikata mumunan ta'adi ga majalisar dokoki da nufin dakatar da ‘yan majalisar daga tabbatar da nasarar Shugaba Biden.

Visual Story 1. Jahrestag der Erstürmung des Kapitols
Hoto: Samuel Corum/Getty Images

Su dai magoya bayan tsohon shugaban na Amirka da suka tafka wan nan danyen aiki a Washington, sun yi amfani ne da damar kafafen sada zumunta na zamani wajen yada manufofinsu da ma watsa abin da suke aikatawa kai tsaye. Abin kuma da masana a harkar sadrwa irin su Regina Lawrence ta jami'ar Oregon da ke Amirkar ke dora laifi a kan jinkirin manyan kafofin watsa labarai wajen bayyana hakikanin abin da ke faruwa.

Zanga-zangar ta birnin Washington dai ta yi sanadin mutuwar magoya bayan Trump din su hudu da ma wani jami'in tsaro, sai kuma wasu mutane 140 da suka jikkata.

An kuma yi Allah wadai da lamarin daga bangarori da dama musamman ma na siyasa a ciki da ma wajen Amirkar.

Visual Story 1. Jahrestag der Erstürmung des Kapitols
Hoto: Jacquelyn Martin/AP Photo/picture alliance

A halin yanzu dai ana ci gaba da bincike kan tsohon Shugaba Donald Trump da ma wasu jiga-jigan magoya bayansa, a kan zargin tunzura wadanda suka aikata wannan aiki, koda yake wasu na da ra'ayin cewa tsohon shugaban na iya samun gaskiya, saboda kura-kuran da aka samu daga kafofin labaran asali da ma na sada zumuntan.

Hukumar binciken manyan laifuka ta Amirkar wato FBI ta tuhumi mutum 727 ta hanyar amfani da hotuna da kemarorin tsaro suka nada da wasu daga shafukan Youtube da ma na wayoyin hannu.

Ana kuma zagin su ne da aikata laifin katse zaman kotu da ma amfani da muyagun makamai.

Sai dai daga cikin wadanda aka yanke wa hukunci, wasunsu an dora musu tara ce da ba ta wuce ta dala 500 biyar ta Amirka ba saboda lalata kadarorin gwamanti, yayin da wasu kuwa suka samu daurin da ya kai shekaru biyar saboda cin zafarin jami'in dan sanda.