1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jirgin ruwa ya kashe mutane a Najeriya

April 14, 2022

Wani jirgnin ruwan fasinja ya nitse a jihar Sokoto inda bayanai suka tabbatar da salwantar rayuka. Mutane 35 ne dai jirgin na ruwa ke dauke da shi a lokacin hadarin.

https://p.dw.com/p/49xF7
Nigeria Bootsunfall
Hoto: AP/picture alliance

Rahotannin da ke fitowa daga jihar Sokoto a Najeriya, na cewa wani hadarin jirgin ruwa, ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutum 29 a yankin karamar hukumar Shagari.

Kwale-kwalen wanda ke dauke da mutane 35 ya nitse ne a kogin Shagari, kuma gwanayen ninkaya sun ceto wasu mutum shida a cewar Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto.

Daga cikin wadanda suka mutun dai har da wasu kananan yara biyar.

Shaidu sun ce galibin wadanda ke cikin kwale-kwalen mata ne, kuma ya zuwa yanzu ba a sanar da musabbabin hadarin ba.

Sai dai ana danganta irin wadannan haduran da daukar mutane da ma kaya fiye da kima, sai kuma rashin matakan ceto fasinja a lokutan ibtila'i.