Hadarin jirgin ruwa ya kashe mutane 24 a Najeriya
September 11, 2023Talla
Jirgin kwale-kwale na dauke da manoma sama da dari da ke tsallaka kogin Neja domin zuwa gonakinsu ta wani bangaren, a jihar Neja. yayin da jirgin ya kife. Garba Salihu,shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar.ya ce a halin yanzu, an gano gawarwaki 24 sannan an ceto mutane 30. Nutsewar jiragen ruwa akan kogunaa Najeriya na faruwa ne saboda yawan lodin jiragen dake yin oba, da rashin kulawarsu ko rashin bin ƙa'idodjin da suka dace.