1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Jaridun Jamus: Ziyarar Scholz a Najeriya

Usman Shehu Usman
November 3, 2023

Jamus na son bude wa 'yan Najeriya masu neman aiki hanyar zuwa Jamus bisa doka, yayin da kuma Jamus ke neman gwamnatin Najeriya ta bada hadin kai a kwaso 'yan Najeriya da suka shiga Jamus ta barauniyar hanya

https://p.dw.com/p/4YOGm
Nigeria | Bundeskanzler Olaf Scholz trifft Präsident Bola Tinubu
Hoto: Nosa Asemota/Nigeria State House/AP/picture alliance

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da yake ganawa da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu a Abuja, ya bayyana bukatar huldar tattalin arziki tsakanin kasashen biyu, sannan ya tabo batun 'yan gudun hijira, sai dai lokacin da shugaban gwamnatin na Jamus ya isa Lagos babban birnin kasuwancin kasar ya ga yawan 'yan Najeriya da ke bukatar fita waje, kuma ya ga halin da wasu daga cikin su da aka dawo da su daga Jamus wadanda ake bai wa horon sanin makamar aiki suke ciki.

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf yayin tattaunawa da 'yan kasuwar Najeriya a Lagos
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf yayin tattaunawa da 'yan kasuwar Najeriya a LagosHoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

A nan shugaban gwamnatin Jamus yace Berlin na matukar maraba da 'yan Najeriya da ke da sana'o'i wadanda ke son zuwa aiki a Jamus. Yanzu haka dai a hukumance akwai 'yan Najeriya kimanin 14,000 da ke zama a Jamus suna neman mafakar siyasa, kuma gwamnatin Jamus ta shirya mayar da su Najeriya dukkaninsu. Sai dai babbar matsalar 12,500 daga cikinsu basu da wata takarda, wanda kuma hakan ke zama abu mai wuya a iya mayar da su gida.

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ita ma ta duba ziyarar shugaban kasar Jamus a gabashin Afirka. Inda ta ce Steinmeier ya roki gafarar Tanzaniya. Shugaban kasar ta Jamus Frank-Walter Steinmeier ya nemi garar ce a lokacin ziyarar aiki da ya kai kasar Tanzaniya, inda yace ya zama wajibi Jamus ta nemi gafara saboda abin da ta aikata wa kasar a zamanin mulkin mallaka

Sarki Charles na Ingila da shugaban Kenya William Ruto
Sarki Charles na Ingila da shugaban Kenya William RutoHoto: Arthur Edwards/The Sun/empics/picture alliance

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung ta duba ziyarar Sarkin Ingila ne Sarki Charles na III a kasar Kenya wanda shi ma batun illar mulkin mallaka ya mamaye ziyarar. Jaridar ta bude labarin da cewa doguwar muhawarar 'yan Mau Mau. Sarkin Burtaniya na III, ya yi bulaguro zuwa tsohuwar kasar da suka yi wa mulkin mallaka a Kenya. Mutane da yawa a wurin suna mamakin yadda zai tunkari wannan batu? wato mummunar murkushe tawayen Mau Mau a shekarun 1950?. 

A wani labarin jaridar die tageszeitung ta duba halin da ake ciki a kasar Sudan, tana mai cewa dakarun RSF sun kwace birane da dama daga hannun sojojin gwamnati. Jaridar ta kara da cewa daga cikin nasarar da RSF ta yi har da kwace biranen da ke zama hedikwatar lardi da wani muhimmin yanki da ke da rijiyaoyin mai wadanda duk suka fada hannun masu adawa da gwamnatin Sudan.

Daya daga cikin babban birnin yankin da suka kwace har da Nyala, babban birnin yankin Darfur kuma nan ne mahaifar jagioran mayakan na RSF wato Mohammed Hamdan Daglo wanda aka sani da Hemidti. Baya ga Nyala haka kuma sun kwace Zalingei, da ke babban birnin jihar Darfur.