1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus tana goyon bayan canji a Masar

February 2, 2011

Bayan sanarwar shugaban Masar, Hosni Mubarak na janyewa daga al'amuran siyasa a watan Satumba, 'yan siyasa a Jamus sun nunar da buƙatar samun canje-canje a ƙasar cikin lumana bakuma tare da bata lokaci ba.

https://p.dw.com/p/109Gt
Magoya bayan jam'iyar yan uwa Musulmi a MasarHoto: picture alliance/ZUMA Press pixel

Shugaba Hosni Mubarak ya ce zai yi murabus daga muƙamin sa, amma ba yanzu-yanzu kamar yadda 'yan adawa a Masar suka nema ba. Wannan dai shine saƙon dake kunshe a jawabin da ya yi wa 'yan ƙasar ranar Talata, kuma shi ne bayanin dake ƙunshe a rahotannin jaridun Jamus yau da safe. Kafofin yaɗa labarai da 'yan siyasa duka sun daidaita a kan cewar canjin da ake buƙata a Masar yana nan tafe, ko da shi ke ba'a san lokacin da wannan canji zai samu ba.

Yanzu dai kaɗan ya rage a kawo ƙarshen wani zamani da aka dade cikin sa a Masar. Bayan mulki na tsawon shekaru 30, shugaba Hosni Mubarak ya sanar da cewar ba zai sake tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasa na gaba ba. To sai dai duk da wannan jawabi, 'yan adawa sun ƙi yarda hakan ya sassauta zukatan su a zanga-zangar da suke kan titunan na Masar saboda neman canjin cikin gaggawa, fiye da yadda shi kansa shugaban yake buƙata. Ministan harkokin wajen Jamus, Guido Westerwelle yayi marhabin da haka.

Guido Westerwelle Pressekonferenz Ägypten
Ministan harkokin wajen Jamus, Guido WesterwelleHoto: AP

Yace girman zanga-zangar dake gudana a biranen Alkahira da Alexandria abu ne da ya ɗauki hankalin mu matuka. Ana iya ganin yadda mutane suka hau kan tituna domin nunar da burin su na tabbatar da yanci amma cikin lumana, abin da gaba ɗaya yake samun goyon baya daga garemu Jamusawa.

Westerwelle yace canjin da ke buƙata wajibi ne ya samu cikin gaggawa, bai kamata a ci gaba da jan lokacin aukuwar sa ba. To sai dai ministan harkokin wajen na Jamus yaki nuna ra'ayin sa sosai a game da ko ci gaba da kasancewar Mubarak a kan mulki yana hana demokraɗiya a Masar, ko kuma abu mafi dacewa shine yayi murabus tun yanzu, maimakon a watan Satumba da yace. Ƙungiyar hadin kan Turai, inji ministan harkokin wajen na Jamus, zata taimaka a aiyukan gina al'amuran shari'a da ilmantarwar siyasa da shirya zaɓuɓɓuka. A nata bangaren gwamnatin Jamus zata tattauna da masu hannu a halin da Masar din take ciki, wato gwamnatin kasar da babban mai adawa da Mubarak, wato Mohammed El-Baradei da kungiyoyi na musulmi. To amma wannan mataki na gwamnati, kamar yadda Jürgen Trittin, kakakin jam'iyar Greens a majalisar dokoki ya nunar, ba zai wadatar ba. Gwamnatin ta Jamus tilas ta matsa lambar ganin Hosni Mubarak yayi murabus ba tare da wani jinkiri ba.

Ägypten Kairo Proteste Demonstrationen Zusammenstöße
Dauki ba dadi tsakanin magoya baya da masu adawa da shugaba Hosni Mubarak a AlkahiraHoto: AP

Yin hakan abu ne mai sauki. Misali, kungiyar hadin kan Turai, a lokacin zaman taron kolin shugabannin kungiyar ranar Jumma'a, domin nazarin taimakon kasafin kudin wasu kashe masu tasowa, tana iya dakatar da taimako ga Masar. Muna iya dakatar da alƙawarin da muka yi na baiwa Masar taimakon makamai na adadin kudi Euro miliyan 75, mu nuna cewar wannan taimako ba za'a bada shi ba sai an sami canje-canje da ake bukata cikin tsari.

A Berlin babu mai sa ran cewar Hosni Mubarak zai kai watan Satumba kamar yadda shi kansa yace yana mulki. To amma duk da munin halin kare hakkin yan Adam da tafiyar da gwamnatin da ba ta democradiya ba, kakakin gwamnati, Steffen Seibert yace bai kamata a kasa ganin wani abin da za'a yaba dashi a mulkin na Mubarak ba.

Yace duk da haka, Masar tayi shekaru 30 tana aiki da yarjejeniyar zaman lafiya da Israila, kuma tayi shekaru masu yawa a matsayin kasa mai sassaucin ra'ayi a yankin gabas ta tsakiya, yankin da shugabannin kasashe masu yara suka maida kansu masu yaki kan kasar Israila. Saboda haka bai kamata a manta da irin gudummuwar da Masar ta bayar ga wannan yanki da kuma duniya baki daya ba.

Mawallafi: Hainer Kiesel/Umaru Aliyu

Edita: Ahmadu Tijani Lawal