1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Obama Mubarak

February 2, 2011

Shugaba Barack Obama na Amirka ya fito fili ya nemi takwaran aikinsa na Masar Hosni Mubarak ya sauka daga karagar mulki kasarsa kamar yadda masu zanga-zanga suka bukata, tun kafin wankin hula ya kai shi ga dare .

https://p.dw.com/p/108xE
Obama da Mubarak a lokacin wata ganawa a White HouseHoto: AP

Mintuna biyar Obama ya shafe a kafofin telebijin na ƙasarsa ya na yin fashin baki, dangane da kunnen uwar shegu da Hosni Mubarak ya ci gaba da yi da kiraye kirayen 'yan ƙasarsa na ya sauka daga karagar mulki. Hasali ma dai sai da yayi amfani da wasu kalaman difolomasiya domin nuna cewa ba ya shisshigi a harkokin wata ƙasa da ba ta tashi ba, kafin ya fito fili ya goyin bayan boren da miliyoyin misirawa ke gudanarwa domin raba Hosni Mubarak da madafun iko. Tuni ma dai Obama ya buga wa shugaban na Masar waya domin bayyana masa ra'ayinsa game da matakan da ya kamata ya dauka domin kwantar da hankali masu boren.

"Ba hurumin wata ƙasa ba ce na tantance wanda ya kamata ya hau kan karagar mulkin Masar. Su da kansu 'yan ƙasar da kansu ne za su iya yanke wa kansu hukunci game da wanda ya fi cancanta ya shugabance su."

Ägypten Mubarak Kairo Proteste Panzer Demonstration 01.02.2011
Dandazon masu bore a alkahira ranar (01.02.2011)Hoto: picture alliance/dpa

Ci gaba da bore na 'yan Masar domin Mubarak ya sauka

Su dai masu zanga-zangar na Masar suke ce babu guda babu ja da baya a yunƙurin da suka fara tun makon da ya gabata, na hambarar da gwamantin Hosni Mubarak da ta shafe shekaru talatin ta na cin karenta ba tare da babbaka ba. Tuni ma suka rigaya suka lashi takobin yin ta a ƙare a ranar juma'a mai zuwa, a inda za su gudanar da gangamin da a taɓa ganin irinsa ba a wannan ƙasa mai dadadden tarihi. Amma shugaba Obama ya haɗa Hosni Mubarak da Allah da ma'aiki da ya kauce jefa ƙasar cikin halin da na sani. Maimakon haka ya hanzarta ya da ƙwallo domin rabuwa da ƙuda. Yayin da a ɗaya hannu ya yaba wa sojojin ƙasar game da halin dattakun da suka nuna, tare da kiran matasa da su san inda kan su ke yi musu ciwo.

"Al'umar Masar musamman matasa daga cikinku, ina so in fito in bayanna muku cewa mun ji kira da ku ka yi. Na yi imanin cewa za ku rungumi kaddara hannu biy-biyu, ku san inda ya kamata ku ɗora ƙasarku."

Mahimmacin ga Mubarak na Sauka cikin girma da arziki

A cewar fadar mulki ta White House, mintuna talatin Obama ya shafe a waya ya na neman shawo kan Hosni Mubarak domin ya sauka, ba tare da haƙarsa ta cimma ruwa ba. Dama kuma ya aika da ambasadar Frank Wisner a matsayin manzon na musamman zuwa birnin Alƙahira domin nuna wa shugaban na Masar alfanun da ke tattare da sauka cikin girma da arzikin, tun kafin wanki hula ya kai ga dare. Daidai da Nicholas Burns jami'in dipolomasiya da ya yi aiki ƙaraƙashin shugaban Bush Junior, sai da ya yaba da wannan yunƙurin na shugaba Obama.

NATO-Botschafter Nicholas Burns NATO Hauptquartier
Nicholas Burns a lokacin da ya ke jakadan Amirka a NATOHoto: AP

"idan da shugaba Obama ya yi gaggawar bayyana matakan da ya ke matsawa Mubarak lamba, da 'yan ƙasar Masar ba za su ɗauki wannan batu da mahimmanci ba. Maimakon haka za su zata cewa ya na neman yaɗa angizon Amirka ne a ƙasarsu. Ina ganin cewa wannan difolomasiyar bayan fagen ya fi mayar da kuɗin sabulu."

Duk da cewa wasu 'yan Amirka na sukan wannan mataki na Obama na matsa wa mubarak lamba domin ya sauka, amma kuma wasu na ganin cewa babban kalubale ne ga manufin ƙetare na gwamanatinsa.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Halimatu Abbas