1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsibirin Lampedusa ya shake da bakin haure

Abdourahamane Hassane SB/AMA
September 18, 2023

Yayin da ya fuskanci dubban bakin haure a 'yan kwanaki a tsibirin Lampedusa na Italiya. Shugabannin Turai na ci gaba da yin kira da a nuna jinkai sabanin kakkausa suka da ‘yan siyasa masu ra'ayin kyamar baki ke yi.

https://p.dw.com/p/4WTBZ
Italiya | Ursula von der Leyen ziyara a Lampedusa tare da Firaminista Giorgia Meloni ta Italiya
Ursula von der Leyen shugabar hukumar Tarayar Turai tare da Firaminista Giorgia Meloni ta ItaliyaHoto: YARA NARDI/REUTERS

Kimanin bakin haure 11,000 ne suka sauka a Italiya tun daga ranar Litinin, yawancinsu a Lampedusa, a cewar ma'aikatar harkokin cikin gida ta Italiya,wadanda suka cika masaukin bakin makil da ke a karkashin kulawar kungiyar agaji ta Red Cross. Kasa da kilomita 150 daga gabar tekun Tunisiya, Lampedusa na daya daga cikin wuraren da bakin haure da ke tsallakawaa tekun Mediterrenean na farko da nufin shiga Turai.

Karin Bayani: Turai: Damuwa kan kwararar bakin haure

Italiya | Bakin huare a Lampedusa
Bakin haure a tsibirin Lampedusa na Italiya Hoto: Cecilia Fabiano/AP Photo/picture alliance

A kowace shekara a irin wannan lokacin na bazara, dubun-dubatar bakin hauren sukan yi kasada don ratsa teku a kan jiragen kwale-kwale marasa inganci galibi don tsallakawa zuwa nahiyar Turai. Wanda kawo yanzu tun daga farkon watan Janairu mutane kusan dubu biyu suka mutu. Kuma Giorgia Meloni ita ce firaministan Italiya wadda ta takaici kan lamarin.

Yanzu haka dai sakamakon yadda wuraran karban bakin a Lenpedusa suka yi cikar kwari. Hukumomin Italiya sun yi jigilar mutane zuwa Siciliya ko wasu tashoshin jiragen ruwa a nahiyar. Kusan bakin haure dubu 126,000 ne suka isa gabar tekun Italiya tun farkon wannan shekara, idan aka kwatanta da shekarar bara wanda ake da baki dubu 65,500 a irin wannan lokacin. Sai dai har yanzu alkaluman ba su zarce na shekara ta 2016 ba, inda sama da mutane dubu 181,000 wadanda yawancinsu 'yan kasar Siriya ne da suka tsere daga yaki suka isa Italiya. Marine Le Pen jagorar jam'iyyar masu kyamar baki ta Faransa ta ce Turai ba za ta ci gaba da karbar bakin hauren ba.

Italiya | Cibiyar kula da bakin haure a Lampedusa
Cibiyar bakin haure ta Lampedusa da ke ItaliyaHoto: Adrian De Loore

Jamus ta aike da wata alama ta gargadin hukumomin Italiya ta hanyar dakatar da karbar masu neman mafaka na son rai, wanda yarjejeniyar Turai ta tanada, ganin yadda Italiya ta ki yin amfani da bangarenta na yarjejeniyar, in ji kakakin gwamnati. Wanda ya ce  sake matsugunin da aka tanada a cikin tsarin hadin kai na Turai na iya komawa a kowane lokaci idan Italiya ta cika hakkinta na mayar da 'yan gudun hijira bisa ga ka'idojin, shugabar Hukumar Tarayyar Turai Ursula Von Der Leyen ta ce lamarin babban kalubale ne.

Tsarin na Turai ya tsara yadda ake mayar da masu neman mafaka daga kasar da suka isa a Tarayyar Turai zuwa wasu kasashe mambobin kungiyar, domin saukaka kasashe kamar Italiya da Girka, wadanda ke zama kofofin shiga yankin Turai. To amma Jamus ta bayyana a wannan makon cewa ta sanar da hukumomin Italiya cewar a ƙarshen watan Agusta cewar an dakatar da ƙaurar da bakin hauran daga Italiya har sai abin da hali ya yi.