1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An halaka jami'an tsaron Najeriya a Mali

December 17, 2022

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi Allah wadai da harin, yana mai jaddada cewa majalisar ba za ta lamunci duk wani farmaki a kan jami'an tsaro ba domin hakan ka iya zama wani laifin yaki.

https://p.dw.com/p/4L5lq
Hoto: picture-alliance/dpa/S. Price

A kasar Mali, an halaka jami'an tsaron Najeriya biyu da ke cikin rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, MDD.

Kwamitin sulhu na Majalisar wanda ya sanar da haka ya ce akwai karin wasu jami'an tsaro hudu da mahara suka jikkata a yayin farmakin da suka kai wa rundunar jami'an tsaron a birnin Timbuktu da ke arewacin Mali.

Shekaru 10 ke nan dai kasar Mali da ke Yammacin Afirka ta kwashe tana fuskantar hare-haren mayakan jihadi, lamarin da ke ci gaba da lakume rayukan jami'an tsaro da fararen hula.