1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yankin zirin Gaza cikin matsi

Abdourahamane Hassane
October 10, 2023

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ko OMS ta yi kira da a bude wata hanyar jin kai zuwa yankin zirin Gaza

https://p.dw.com/p/4XMfM
Hoto: Ronen Zvulun/REUTERS

sojojin Isra'ila sun rufe hanyoyin shiga yankin Gaza  tare da yi musu ruwan bama-bamai bayan hare-haren Hamasda suka yi sanadiyyar  mutuwar daruruwan rayuka a Isra'ilar. Ana buƙatar hanyar jin kai don isar da muhimman kayayyakin kiwon lafiya ga jama'a, in ji mai magana da yawun hukumar a wani taron Majalisar Dinkin Duniya da ake yi a  Geneva, wanda ya ce suna  tattaunawa da bangarori dabam-dabam domin samun hanyar akewa da kayayyakin.Yanzu hada dai Isra'ilan ta yi wa yankin na zirin Gaza kawanya kana tana yi masa ruwan wuta sannan ta cire ruwan fomfi na sha da wutar lantarki a yankin. Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewar matakin da israilan ta dauka yaharamta daga dokokin kasa da kasa.