1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIsra'ila

Mutane da dama sun halaka a Isra'ila da Zirin Gaza

October 8, 2023

Yayin da ake ci gaba da gwabza fada tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas mai iko da Zirin Gaza kungiyar Hizbullah da ke Lebanon ta kai wa Isra'ilar wasu jerin hare-hare.

https://p.dw.com/p/4XFqq
Mutane da dama sun halaka a Isra'ila da Zirin GazaHoto: MAHMUD HAMS/AFP

Alkaliman baya-bayan nan na nunar da cewa yakin da ya barke tsakanin Zirin Gaza da Isra'ila a ranar Asabar (07.10.2023) biyo bayan farmakin da kungiyar Hamas ta kaddamar ya yi ajalin sama mutane 200 tare da jikkatar wasu sama da 1.000 a bangaren Isra'ila a giddiddigar da sojojin kasar suka fitar.

A yankin Zirin Gaza kuwa inda sojojin Isra'ila suka kutsa domin yin martani ta hanyar hare-hare ta sama, hukumomin Hamas da ke iko da karamin yankin tun shekarar 2007 sun sanar da mutuwar mutane 232.

Karin bayani: Isra'ila ta lashi takobin ramuwar gayya mai zafi kan Hamas

To sai dai a daren Asabar wayewar Lahadi, dakarun Isra'ila sun ci gaba da yin luguden wuta a kan wasu gine-gine da ke Zirin Gaza da suka siffanta da tungar 'yan ta'adda, yayin da ita ma kungiyar Hamas ke ci gaba da cilla wa Isra'ilar rokoki kamar yadda kamfanin dillacin labarun Faransa na AFP ya ruwaito.

Karin bayani: Isra'ila da Gaza sun kasa tsagaita wuta

A  yayin da ake gwabza fadan Firaminstan Isra'ila Benjamin Netanyahou ya mika tayi ga 'yan adarwa da su zo a kafa gwamnatin hadin gwuwa domin dinke duk wata baraka a daidai lokacin da kasar ke cikin barazana.

A daya gefe kuma rundunar sojojin Isra'ila ta ce ta kai hari a Kudancin kasar Lebanon a safiyar Lahadi (08.10.2023) a matsayin martani ga wasu jerin harbe-harbe da ta ce na fitowa daga yankin i zuwa cikin Isra'ilar.

A cikin wata sanarwa rundunar ta ce tana ci gaba da yin luguden wuta wa yankin na Lebanon da ta ce harbe-harben na fitowa daga can sai dai ba ta yi ba karin bayani kan irin makaman da ta ce an harbo wa kasar.

To amma a cikin wata sanarwa kungiyar Hizbullah ta bayyana cewa ta kai hari kan wasu barikoki uku na sojojin Isra’ila a wani yanki da ke kan iyakar kasar ta hanyar amfani da rokoki da kuma makamai masu linzami.

Kasashen duniya dai na ci gaba da yin Allah wadai da wannan sabon yaki da ya barke, suna masu kiran bangarorin biyu da su kai zucciya nesa.

Karin bayani: Duniya na Allah wadai da sabon rikicin Hamas da Isra'ila