1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Rikice-rikiceGabas ta Tsakiya

Gaza: Isra'ila ta kubutar da 'yan kasarta a Rafah

February 12, 2024

Isra'ila ta kubutar da mutane biyu da mayakan Hamas su ka yi garkuwa da su a Rafah da ke Gaza, a daidai lokacin da ma'aikatar lafiyar Gaza ta ce mutane 52 ne suka mutu ciki har da kananan yara a hare-haren Isra'ilan.

https://p.dw.com/p/4cHln
Hoto: Ronen Zvulun/Reuters

A sanarwar da ma'aikatan tsaron Isra'ila ta fitar ta ce mutanen biyu Fernando Simon Marman da  Louis Har, na daga cikin mutanen da mayakan Hamas suka yi garkuwa da su a ranar 7 ga watan Oktoba.

Sojojin Isra'ila na ci gaba da nausawa zuwa cikin birnin Rafah da ke kan iyakar Masar, birnin da daruruwan 'yan gudun hijra suka samu mafaka daga hare-haren Isra'ila.

Karin Bayani:Isra'ila ta umurci a kwashe fararen hula daga garin Rafah

Halin da ake ciki a yankin da kuma bukatar shigar da kayan agaHamas ta gargadi Isra'ila a kan shiga Rfahjin gaggawa ya sanya hukumomi da gwamnatocin kasashen duniya ciki har da babbar kawar Isra'ilan wato Amurka ci gaba da nuna damuwa kan fadada kai hare-haren Isra'ila yankin na Rafah.

Karin Bayani:Saudiyya ta bukaci a dakatar da Isra'ila daga shiga Rafah

Duk da matsin lamba daga kasashen duniya, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, na ci gaba da jaddada kai farmaki yankin na Rafah, kamar yadda ya bada umarni ga sojojin Isra'ila da su kasance cikin shiri na shiga birnin.

Karin Bayani:Masar: Adawa da kwararar 'yan gudun hijira

Hare_haren Isra'ailan na daren litinin 12 ga watan Fabrairu, 2024, ya lalata gidaje akalla 14 da masallatai 3 a Rafah, acewar hukumomin yankin.