1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta kaddamar da mummunar farmaki a Jenin

August 29, 2024

Sojojin Isra'ila sun kaddamar da farmaki mafi muni a yankin Jenin da ke gabar yamma da Kogin Jordan, a ci gaba da yakin da Isra'ila ta ke gwambzawa da kungiyar Hamas.

https://p.dw.com/p/4k2Cs
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu
Firaministan Isra'ila, Benjamin NetanyahuHoto: Ronen Zvulun/AP Photo/picture alliance

Harin na Jenin na kasancewa farmaki mafi muni a watannin da aka shafe ana yaki tsakanin Isra'ila da Hamas a zirin Gaza, tun bayan harin da mayakan Hamas suka kaddamar kan Isra'ilan a ranar 7 ga watan Oktoba.

Karin bayani: Hare-hare Isra'ila sun yi ajalin fararen hula a birnin Jenin

Mai magana da yawun sojin Isra'ila, Laftanal Kanal, Nadav Shoshani, ya ce sojojin Isra'ila sun shiga yankin Jenin da ke gabar yamma da kuma Tulkarem har ma da yankin Al-Faraa, da ya kasance sansanin 'yan gudun hijrar da ke arewacin Gabar Yamma a lokacin yakin Gabas ta Tsakiya a shekarar 1948.

Karin bayani: Dakarun Isra'ila sun janye daga Jenin

Hukumomin Falasdinu sun  ce harin na Jenin ya halaka akalla mayakan Hamas guda goma, tare kuma da wasu mutanen guda hudu. Gwamnan Jenin Kamal Abu al-Rub, ya gabatar da jawabi a gidan radiyon Falasdinu inda ya ce dakarun Isra'ila sun yiwa birnin kawanya tare da dakile hanyoyin zuwa asibiti da kuma na shige da ficen birnin.