1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta halaka Falasdinawa 200 kafin ta kubutar da hudu

June 9, 2024

A daidai lokacin da Isra'ila ke fuskantar matsin lamba na dakatar da yakin Gaza, Hamas ta ce sojojin Isra'ila sun halaka sama da mutum 200 kafin su kai ga kubutar da mutum hudu Gaza, yayinda wasu da dama suka jikkata.

https://p.dw.com/p/4gpTn
Sansanin 'yan gudun hijra na al-Nuseirat da ke Gaza da Isra'ila ta yiwa luguden wuta
Sansanin 'yan gudun hijra na al-Nuseirat da ke Gaza da Isra'ila ta yiwa luguden wutaHoto: Jehad Alshrafi/AP Photo/picture alliance

A jiya asabar, Isra'ila ta yi shelar kubutar da mutum 4 daga cikin wadanda kungiyar Hamas ta yi garkuwa da su a gidan rawa na Nova da ke Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba, wanda hakan ya haifar da mummunar yakin da ake gwabzawa tsakanin bangarorin biyu.

Kayan tarihi: Amurka da Burtaniya da Jamus na fatan dakatar da yakin Gaza 

Sanarwar Hamas na mutuwar fararen hular na zuwa ne a daidai lokacin da Cibiyar Tattara Bayanan Tsaron Amurka ta sanar da cewa an fara shigar da kayayyakin agajin jinkai a zirin Gaza tare kuma da sake gina tantuna na wucin-gadi a zirin domin sake tsugunar da dubun dubatar 'yan gudun hijrar da suka rasa muhallansu tare kuma da samar da cibiyar tattara kayayyakin agajin jinkan ga fararen hula.

Kayan tarihi:  Kotu ta umarci Isra'ila ta dakatar da yaki a kudancin Gaza

A gefe guda, Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya ce sun rasa ma'aikata 135 a yakin na Gaza, adadi mafi girma da aka taba kashe ma'aikatan majalisar a yaki gudu, adon haka akwai bukatar kawo karshen wannan tashin hankalin.