1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIsra'ila

Isra'ila ta ce babu batun sakin fursunoni kafin ranar Juma'a

November 23, 2023

Isra'ila ta ce ana ci gaba da tattaunawa kan batun tsagaita kai hare-hare a Zirin Gaza, sai dai ba za kai ga sakin fursunonin da ake rike da su ba kafin ranar Juma'a.

https://p.dw.com/p/4ZL6l
Hotunan wasu da Hamas ke garkuwa da su
Hotunan wasu da Hamas ke garkuwa da suHoto: Debbie Hill/UPI Photo/Newscom/picture alliance

Wannan dai sanarwa ce da ke zuwa bayan rahotannin farko sun nuna yiwuwar sakin 'yan Isra'ila da kungiyar Hamas ke rike da su a wannan Alhamis.

Babban mai ba da shawara kan harkokin tsaro a Isra'ila, Tzachi Hanegbi bai yi wani bayani ba a kan dalilin jinkirin da aka samu, kuma babu tabbaci nan take kan yaushe yarjejeniyar tsagaita wuta ta wucin gadi ke fara aiki.

Sai dai tasahar watsa labarai mallakin gwamnatin Isra'ila, ta ruwaito cewa za a samu jinkirin sa'o'i 24 a yarjejeniyar da aka cimma.

Tashar da ake kira Kan, ta ce an samu akasin ne, saboda Hamas da kasar Qatar da ta shiga tsakani ba su sanya hannu kan takardar yarjejeniyar ba.

Wani jami'in gwamnatin Isra'ila ta tashar ta ambato, ya ce yana da kwarin gwiwar cewa yarjejeniyar dai za ta yi aiki.

A jiya Laraba ne ma kasar ta mince a hukumance kan cewa za a fara tsagaita wuta a yakin na Gaza na kwanaki hudu, inda kungiyar Hamas za ta sako ISra'ilawan da ke hannunta mutum 50, yayin kuma da Isra'ila za ta saki falasdinawa fursunoni su 150.